Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'addan ISWAP a Sansaninsu, an Kashe Mayaka da Dama

Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'addan ISWAP a Sansaninsu, an Kashe Mayaka da Dama

  • Dakarun sojoji sun kai harin sama kan mayaƙan ISWAP a wani samamen jirgi mara matuƙi a yankin Kila Bariya
  • Hare-haren sun yi sanadiyyar lalata babura sama da 30 da 'yan ta'addan suka tanada domin ayyukan ta’addanci
  • Harin ya lalata ma’ajiyar abinci ta ISWAP da ke ɗauke da wake da sauran kayan abinci, yayin da aka kuma hallaka mayaka da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Sabon binciken barnar da aka yi a fagen daga ya tabbatar da cewa an hallaka sama da mayaƙan ISWAP 20.

An hallaka mayakan a wani harin jirgi mara matuƙi da bangarrn rundunar sojojin sama ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta kai a Kila Bariya, a yankin Kudancin Tafkin Chadi.

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP
Dakarun sojoji a fagen daga Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Ya mutu yana kaina"; Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar Janar Abacha

Majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa an kai harin ne a ranar Talata, 21 ga Yuli, bayan samun sahihan bayanan sirri kan kasancewar mayaƙan ƙungiyar da kayayyakin yaƙi masu muhimmanci a wani muhimmin sansanin ajiye kayan aiki da tattara mayaƙa na ’yan ta’addan.

Binciken baya-bayan nan ya nuna cewa wasu ’yan ta’addan da dama sun samu munanan raunuka, yayin da aka lalata babura sama da 30, mafi yawansu sababbi ne kuma an tanade su ne domin ayyukan ta’addanci.

An lalata ma’ajiyar abinci

Binciken ya kuma nuna cewa harin ya lalata wata babbar ma’ajiyar abinci ta ISWAP da ke ɗauke da dimbin wake da sauran kayan abinci da ake zargin an kwace ko kuma an karɓe su da ƙarfi daga al’ummomin manoma a faɗin yankin Kudancin Tafkin Chadi.

Majiyoyin soji sun bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin manyan hare-haren da aka kai cikin nasara a makonnin baya-bayan nan, inda suka ce ya yi wa ikon ƙungiyar na zirga-zirga, samar da kayan aiki da kuma ci gaba da ayyukanta babban lahani.

Wata babbar majiyar soji ta ce:

“Lalacewar baburan za ta rage matuƙar ikon ’yan ta’addan na kai hare-haren bazata cikin sauri da tura ƙarin mayaƙa a mawuyacin yanayin ƙasar Tafkin Chadi, yayin da asarar tarin abincin za ta ƙara raunana ikonsu na ci gaba da ayyuka na tsawon lokaci.”

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi babban kamu a Borno, sun cafke ɗan kasar waje dake tallafawa ISWAP

Sojoji na rage tasiri 'yan ta'addan ISWAP

Ana sa ran nasarar harin za ta sauya yanayin ayyukan ’yan ta’adda a yankin Kudancin Tafkin Chadi, musamman a yankunan ƙananan hukumomin Marte, Ngala da Dikwa, inda ISWAP ke ci gaba da ƙoƙarin sake haɗa mayaƙanta da kuma ƙara faɗaɗa tasirinta.

Sojojin Najeriya na ci gaba da kai hare-haren sama masu ƙarfi a ƙarƙashin Operation Hadin Kai kan 'yan ta'adda.

Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'an tsaron na haɗa sahihan bayanan leƙen asiri, sa ido na dindindin da kuma hare-haren da ake kai wa kan sansanonin ’yan ta’adda domin hana ’yan tada ƙayar baya ’yancin zirga-zirga tare da tarwatsa hanyoyin jagoranci, samar da kayan aiki da kuma ayyukansu.

Sojoji sun dakile harin ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun dakile yunƙurin sace ɗalibai da dama da ƴan ta’addan ISWAP ne suka yi a jihar Borno.

Sojojin sun dakile harin 'yan ta'addan ne a makarantar Federal Government Girls College (FGGC), Monguno, inda suka ceto ɗalibai 46.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng