Bayan Shekara a APC, Sanata Ya Koma Tsohuwar Jam'iyyarsa
- Sanatan jam'iyyar adawa, Olubiyi Fadeyi ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC watanni 12 da sauya shekarsa saboda an gaza cika alkawari
- Sanatan mai wakiltar mazabar Osun ta Tsakiya ya bayyana cewa akwai rashin dimokuraɗiyya da kuma samun sabani da shugabancin jam'iyyar a Osun
- Duk da sauya jam'iyya, Fadeyi ya jaddada cewa har yanzu yana goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manufofin gwamnatin sa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Sanatan da ke wakiltar mazabar Osun ta Tsakiya, Olubiyi Fadeyi, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC shekara guda kacal bayan shiga jam'iyyar.
Fadeyi ya bayyana hakan ne cikin wasiƙar murabus da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Sanatan ya ce ya shiga APC ne da kyakkyawar niyya domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a yankin mahaifarsa.
Yadda Sanatan PPDP ya koma APC
The Nation ta rawaito cewa Sanata Olubiyi Fadeyi ya ce ya koma APC bayan an tabbatar masa cewa zai samu tikitin takarar Sanata na jam'iyyar a zaɓen 2027.
Sanatan ya ce an sanar da shi cewa Shugaba Tinubu ya amince da ba shi tikitin komawa takara, kuma an isar da wannan matsaya ga shugabannin APC na jihar Osun.
Sai dai ya zargi shugabannin APC na jihar da karya yarjejeniyar da aka yi, yana mai cewa ba su gudanar da tsarin sasanci da kuma zaɓen fidda gwani cikin gaskiya ba, lamarin da ya haifar masa da rashin amincewa da shugabancin jam'iyyar.
APC ta fusata Sanata kan takara
Fadeyi ya bayyana cewa abin ya fi ba shi takaici ne ganin yadda wasu Sanata da mambobin Majalisar Wakilai uku da suka sauya sheƙa tare da shi suka samu tikitin komawa takara, amma shi aka hana ba tare da wani bayani ba.
Ya ce hakan ya bar tambayoyi masu yawa, musamman duba da cewa shi ne ya kayar da Sanatan APC mai ci daga Osogbo a babban zaɓen 2023, abin da ya nuna yana da karɓuwa a wajen al'ummar mazabarsa.

Source: Twitter
Sanatan ya ce yana sa ran biyayyarsa ga jam'iyyar da kuma irin gudummawar da ya bayar za su sa a yi masa adalci, amma hakan bai faru ba.
Fadeyi ya bar PDP zuwa APC a watan Yulin shekarar da ta gabata, inda ya danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida, shari'o'i da kuma rashin jagoranci a PDP.
Jigon APC ya soki yan takarar NDC
A wani labarin, kun ji cewa wani jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Iliyasu Musa Kwankwaso ya ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su da ƙarfin lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da ke tafe.
Ya yi zargin cewa Rabiu Kwankwaso na iya kasancewa da wata manufa ta siyasa daban duk da kasancewarsa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, lokaci ne kawai zai fito da cikakkiyar manufarsa.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma ce Arewa na ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ayyukan da gwamnatinsa ke aiwatarwa da ke kara kawo ci gaba a sassa daban-daban na shiyyar.
Asali: Legit.ng

