Matashi Ya Kalubalanci Ministan Tsaro, Ya Ƙaryata Shi game da Kalamansa kan Abinci Sojoji

Matashi Ya Kalubalanci Ministan Tsaro, Ya Ƙaryata Shi game da Kalamansa kan Abinci Sojoji

  • Mai fafutuka a jafafen sada zumunta ya musanta zargin Ministan Tsaro Christopher Musa kan sojoji
  • Matashin ya bayyana cewa bai umarci sojoji su cire nama daga abincinsu domin ɗaukar bidiyo yayin cin abinci
  • Ya ce bai da wani iko kan sojoji, yana mai cewa wasu daga cikinsu ne suka tuntube shi domin bayyana damuwarsu kan walwala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai fafutuka a kafafen sada zumunta, Mark Justice ya kalubalanci Hafsan sojoji, Janar Christopher Musa mai ritaya.

Matashin wanda aka fi sani da Justice Crack, ya musanta zargin Christopher Musa, cewa ya umarci sojojin Najeriya su cire nama daga abincinsu.

Matashi ya kalubalanci kalaman hafsan sojoji
Ministan tsaro a Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Martanin nasa ya biyo bayan wata hira da Ministan Tsaron ya yi a News Central, inda ya ce bidiyon da ya nuna ƙarancin abincin sojoji an shirya shi ne.

Kara karanta wannan

Sheikh Guruntum ya ba da mamaki, ya gargadi masu yi masa kirari

Ministan ya yi magana kan kushe abincin sojoji

Ministan ya ce abincin sojojin ya ƙunshi nama da sauran kayan abinci, amma ya zargi Justice Crack da umartar su cire waɗannan abubuwa domin yaudari jama'a.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Justice Crack ya ce wannan zargi ƙarya ne kuma yana bata masa suna ba tare da wata hujja ba.

Ya ce bai taɓa umartar wani soja ya cire nama ko wani abu daga abincinsa ba, yana tambayar wane iko yake da shi kan jami'an soja.

Justice Crack ya bayyana cewa ba shi ne ya nemi sojojin ba, sai dai wasu daga cikinsu ne suka tuntube shi suna bayyana damuwa kan walwala da yanayin aikinsu.

Ya ce ya wallafa bidiyon ne domin jawo hankalin hukumomin soja su inganta walwala da yanayin rayuwar maza da mata masu kare Najeriya, cewar Punch.

Ya ƙara da cewa kalaman Ministan Tsaro na iya bata masa suna a idanun jama'a, yana jaddada cewa fafutukarsa ta ta'allaka ne kan tabbatar da gaskiya, inganta walwalar jami'an tsaro da kuma kyakkyawan shugabanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya

A watan Mayu, an gurfanar da Justice Crack a kotu tare da tsare shi saboda wani bidiyo da ya wallafa kan zargin ƙarancin abincin sojojin Najeriya.

Ana tuhumarsa da laifukan da suka shafi amfani da kafafen intanet, ciki har da zargin ya wallafa bayanan da hukumomi suka ce ƙarya ne domin haifar da ƙiyayya da rashin jituwa, wanda ya saba wa Dokar Laifukan Yanar Gizo ta Najeriya.

Barazanar da ƴan bindiga suka yi wa sojoji

An ji cewa ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce 'yan bayyana dalilin da ya hana jami'ai su fafata da yan bindiga da suka yi garkuwa da daliban jihar Oyo.

A makonnin da suka wuce, yan bindiga sun shiga jihar inda suka yi awon gaba da dalibai da malamansu a makarantu daban-daban na Oyo, aka nutsa da su cikin daji.

Da ya ke bayani a kan dalilin da ya sa har yanzu aka gaza ceto su, Christopher Musa ya bayyana cewa akwi dalili, kuma ana bakin kokari wajen kwato lafiya lau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.