Mutuwa ba Ta Bar Kowa ba: Tsohon Sanata a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekaru 76

Mutuwa ba Ta Bar Kowa ba: Tsohon Sanata a Najeriya Ya Rasu Yana da Shekaru 76

  • An shiga jimami a jihar Ondo bayan sanar da mutuwar tsohon sanata a Najeriya wanda aka ce ya bayar da gudummawa sosai
  • Tsohon sanatan Ondo ta Kudu, Omololu Samuel Meroyi, ya rasu yana da shekara 76 a duniya sai dai ba a faɗi sanadin mutuwar ba
  • Marigayin ya wakilci Ondo ta Kudu a Majalisar Dattawa tsakanin 1999 da 2003, bayan ya fara siyasa a AD kafin daga bisani ya koma PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Akure, Ondo - Tsohon Sanatan da ya wakilci Ondo ta Kudu a Majalisar Dattawa, Omololu Samuel Meroyi, ya rasu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayi tsohon sanatan ya bar duniya yana da shekara 76 a duniya.

Tsohon sanata a Najeriya ya bar duniya
Taswirar jihar Ondo da aka rashin tsohon sanata. Hoto: Legit.
Source: Original

A tabbatar da rasuwar tsohon sanata a Ondo

Ɗan'uwansa, Meroyi Yomi Charles, ya tabbatar wa Sahara Reporters rasuwarsa a ranar Laraba, yana mai cewa tsohon ɗan majalisar ya rasu ne da safiyar ranar.

Kara karanta wannan

Duniya rumfar kara: Basarake ya rasu a Bauchi kwana 6 da naɗa shi sarauta

Sai dai Charles bai bayyana musabbabin rasuwar tsohon sanatan ba lokacin da yake tabbatar da labarin.

An fara zaɓen Meroyi zuwa Majalisar Dattawa a shekarar 1999 a ƙarƙashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), inda ya wakilci mazabar Ondo ta Kudu.

Daga bisani ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya inda ya ci gaba da harkokinsa na siyasa.

Tsohon sanata daga Ondo ya rasu
Tsohon sanata daga jihar Ondo, Omololu Samuel Meroyi. Hoto: Ondo South TV.
Source: Facebook

Yaushe aka haifi marigayi tsohon sanatan?

An haifi Meroyi ne a ranar 1 ga Janairu, 1950, ya samu digirin digirgir na biyu (MSc) a fannin tattalin arziki daga 'London School of Economics'.

Kafin zamansa sanata, an zaɓe shi zuwa Majalisar Wakilai a shekarar 1983, inda ya fara taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.

Bayan kammala wa'adinsa a Majalisar Tarayya, ya ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa, sannan ya zama mataimakin shugaban ƙasa na yankin Kudu maso Yamma a ƙungiyar tsofaffin sanatocin Najeriya.

Baya ga siyasa, an ce marigayin kwararren mai ba da shawara ne kan harkokin gudanarwa. Sannan ya taba zama shugaban kamfanin roba na 'Araromi Rubber Estates'.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi: Daya daga cikin manyan limaman masallaci ya rasu a Kwara

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayani kan yadda ya rasu ko kuma shirye-shiryen jana'izarsa ba.

Ƙungiya ta yi ta'aziyyar rasuwar tsohon sanatan

Shugaban kungiyar Achievers Progressive Group, Adesulere Ibukun ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon sanatan tare da ba iyalansa hakuri a wani rubutu a Facebook.

Ibukun ya bayyana cewa tabbas an yi rashin mutumin kirki wanda maye gurbinsa zai yi matukar wahala duba da irin gudunmawar da ya bayar ga al'umma.

Tsohon sanata a Najeriya ya rasu

Mun ba ku labarin cewa an tabbatar da rasuwar tsohon sanatan da ya wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, John Kojo-Brambaifa a wani asibiti a Abuja.

Gwamna Douye Diri ya nuna damuwarsa da alhini bisa rasuwar tsohon sanatan, wanda ya bayyana da jajirtaccen mutum wanda ya taimaki jama'a.

A madadin gwamnati da al'ummar Bayelsa, Gwamna Diri ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da sauran al'ummar kauyen Agbere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.