Yadda Alkalin CCT Ya Casa Tinubu, Saraki da Sauran Manya kafin Ya Kare a Kurkuku

Yadda Alkalin CCT Ya Casa Tinubu, Saraki da Sauran Manya kafin Ya Kare a Kurkuku

Abuja - A ranar Alhamis 9 ga watan Yuli 2026, Kotun tarayya mai zama a Maitaima a Abuja ta aika Danladi Umar zuwa gidan gyaran hali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Shugaban kotun da'ar ma'aikatan zai zauna a gidan kurkukun ne saboda wasu zargi har hudu da ake yi masa na rashin gaskiya da cin amanar ofishinsa.

Danladi CCT
Bola Tinubu, Bukola Saraki da Alkalin CCT, Danladi Umar a tsakiya Hoto: Getty Images/OfficialEFCC
Source: UGC

Alkalin CCT, Danladi Umar ya tafi gidan maza

Hukumar EFCC ta fitar da jawabi a shafinta na Facebook, ta ce ta yi karar Danladi Umar a gaban Mai shari’a Peter Kekemeke a kotun tarayya.

Sa’ilin da yake alkalanci a kotun sa ta CCT mai alhakin shari’a game da kadarorin masu rike da mukaman gwamnati, Danladi Umar ya shahara.

A sakamakon karar da aka shigar a gabansa, wasu sun rasa mukamansu a Najeriya, wasunsu kuma akalla sun samu mummunan tabo wajen jama’a.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Kotu ta zauna kan shari'ar shugaban Miyetti Allah kan tuhume tuhume

Dazu Daily Trust ta yi waiwaye, ta nemo manyan shari’o’in da Danladi Umar ya yi a kotun CCT a baya tun daga kan shugaban kasa mai-ci a yau.

CCT: Manyan da suka je gaban Danladi Umar

1. Walter Onnoghen

A farkon 2019 aka gurfanar da Walter Onnoghen a gaban kotun CCT bisa zargi shida da suka shafi yin karya lokacin gabatar da arzikin da ya mallaka.

Abin da ya ja hankalin ‘yan Najeriya lokacin shi ne wanda ake zargi shi alkalin alkalai na kasa.

Ana cikin wannan shari’a ne Walter Onnoghen ya yi murabus amma duk da haka kotun ta same shi da laifi kuma ta bada shawarar a tunbuke shi.

CCT ya kuma yi hukunci cewa a hana alkalin rike mukami na tsawon shekaru 10 sannan ta yi marni a karbe dukiyoyin da aka yi shari’ar a kansu.

2. Bukola Saraki

Tsohon gwamnan Kwara ya sha wahala a hannun Danladi Umar a CCT. Bukola Saraki ya fuskanci shari’a mai tsawo a tarihi da ya je kotun daga 2015.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta tura tsohon shugaban CCT ta Najeriya gidan yari a Abuja

Jim kadan bayan zama shugaban majalisar dattawa sai gwamnati ta zarge shi da yin karya lokacin bayyana arzikin da ya mallaka, an yi shekaru uku a kotu.

Sai a Yunin 2018 ne kotun ta CCT ta kori karar saboda masu tuhma ba su kawo hujjoji ba. Sai da shari’ar ta kai har Kotun koli kuma Saraki ya yi galaba.

3. Sylvester Ngwuta

Shi ma Alkali Sylvester Ngwuta ya san halin Danladi Umar domin ya fada hannunsa a shekarar 2017 lokacin da jami’an DSS suka dura cikin gidansa.

An samu kudi masu yawa a cikin gidan alkalin na kotun koli don haka shi ma aka zarge shi da irin wannan laifi, amma dai Danladi Umar ya kori kararsa.

Kotun CCT ta ce za a saurari shari’a ba har sai NJC ta same shi da laifi ta fara ladabtar da shi tukuna. Jaridar The Nation ta kawo labarin a lokacin.

4. Godsday Orubebe

Godsday Elder Orubebe ya bayyana a gaban Danladi Umar a kotun shi tun shekarar 2016 bisa zargin kin bayyana ya mallaki wani gida a Asokoro.

Kara karanta wannan

Bincike ya shiga matatun mai, EFCC ta kai tsohon shugaban matatar Fatakwal kotu

Lokacin da za a nada shi ministan harkokin Neja-Delta, gwamnati ta ce bai nuna yana da wannan dukiya ba, saboda haka aka nemi a hukunta shi a kotu.

A karshen shari’ar da ICPC, alkalin CCT ya same shi da laifi saboda an samu sunan shi a takardun gidan. A 2017 kotun daukaka kara ta rusa wannan hukunci.

5. Bola Tinubu

Shi kan sa Mai girma Bola Ahmad Tinubu ya san da zaman kotun CCT domin kuwa a shekarar 2011 an yi kararsa saboda zargin aikata laifuffuka a ofis.

An tuhumi Tinubu da amfani da asusun kudin kasashen waje lokacin da yana gwamna a jihar Legas. Sai dai kafin shari’ar ta yi nisa kotu ta wanke shi.

Kotu ta ce ba a iya gamsar da ita tsohon gwamnan ya mallaki kudin wajen da ake magana a kai ba. Daga baya Premium Times ta rahoto yadda aka hakura da karar.

Kotu ta tura Danladi Umar gidan yari

Ana da labari babbar kotun Tarayya da ke Abuja (Maitama) ta ba da umarnin a tsare tsohon shugaban Kotun Da'a ta Kasa, Danladi Umar, a kurkuku.

Kara karanta wannan

ICPC za ta gurfanar da tsohon ministan Tinubu da aka samu da takardun bogi

Alkalin kotun na CCT zai zauna gidan yarin Kuje, bayan gwamnatin tarayya ta hannun EFCC ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume hudu na rashawa.

Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Umar ya musanta su. Lauyan gwamnati ya nemi a tsare shi, yayin da lauyoyinsa suka nemi a ba shi beli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng