Iran Ta Tayar da Gobara a Sansanin Sojin Amurka bayan Sakin Bama Bamai
- Dakarun IRGC na Iran sun ce sun kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait da Jordan a wani sabon mataki na rikicin da ke tsakanin ƙasashen
- Iran ta yi ikirarin lalata makaman soja, tsarin kariyar makamai masu linzami da wuraren ajiyar jiragen yaƙi tare da kashewa da jikkata sojojin Amurka
- Yayin da Iran ke ci gaba da kai hare-hare, 'yan Republican a Majalisar Wakilan Amurka sun fara yunkurin amincewa da kasafin kuɗin dala biliyan 95 don yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran, Iran – Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun sanar da cewa sun kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Kuwait da Jordan.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun kasance martani ga farmakin da Amurka ta kai kan wasu muhimman cibiyoyin sadarwa na Iran.

Kara karanta wannan
Trump ya ji zafin kisan sojojinsa da Iran ta yi, zai karbi gawarwakinsu a wani biki a Amurka

Source: Getty Images
Anadolu Agency ta rahoto cewa IRGC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da gidan talabijin na gwamnatin Iran (IRIB) ya wallafa
Abin da Iran ta ce ta lalata
A cewar IRGC, ta kai hari kan sansanin sojin Ali Al Salem da ke Kuwait, inda ta ce ta lalata wani babban wurin ajiyar kayan aikin soja, tsarin kariya daga makamai masu linzami na Patriot da kuma wani waje da ake ajiye jiragen yaƙi marasa matuƙa na MQ-9.
Har ila yau, ta yi ikirarin kai hari sansanin Udairi, inda ta ce ta lalata wuraren kwanan sojojin Amurka, wurare guda biyu na jirage masu saukar ungulu tare da jikkatawa da kashe wasu sojojin Amurka, ko da yake ba ta bayyana adadinsu ba.
IRGC ta ƙara da cewa ta kai hari kan hasumiyar sadarwa domin mayar da martani ga hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin sadarwa a cikin Iran.
Ta kuma jaddada cewa hare-haren da ta kai a Kuwait sun shafi wuraren da sojojin Amurka ke amfani da su ne kawai, ba wai sun saba wa ikon mallakar ƙasar Kuwait ko mutuncin yankinta ba.

Source: Getty Images
An kai hari a Jordan
Sanarwar ta kuma ce dakarun IRGC sun kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Jordan, inda suka yi ikirarin lalata na'urar gano hare-hare ta tsarin kariya na THAAD, tsarin Patriot da kuma na'urar C-RAM.
Bugu da ƙari, Iran ta ce hare-haren sun haddasa gobara a tankunan adana mai, wurin ajiyar kayan aikin jirage masu saukar ungulu da kuma cibiyar gyaran jiragen.
Ga bidiyon harin da the Cradle ta wallafa a X:
Damuwar da Trump ya nuna
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana mutuwar wasu sojojin Amurka a Jordan a matsayin babban abin takaici.
Trump ya ce sojojin sun rasa rayukansu ne yayin da suke kare muradun Amurka da hana Iran mallakar makamin nukiliya, bayan Iran ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka a Jordan.
Hakan na zuwa ne yayin da Iran ke cigaba da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya, musamman Kuwait da Jordan.
Asali: Legit.ng
