Wasiyyar da Trump Ya Bari idan Iran Ta Samu Nasarar Kashe Shi
- Donald Trump da ke shugabantar Amurka ya bayyana abin da ya sanar da jami'ai idan har Iran ta samu nasarar raba shi da duniya
- Shugaban na Amurka ya ce Tehran ta dade tana neman kashe shi tun bayan mutuwar Janar Qasem Soleimani
- Kalaman sun zo ne bayan an nuna alluna dauke da rubuce-rubucen da ke kira da a kashe Trump a wajen jana'izar jagoran Iran, Ali Khamenei
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya riga ya bayar da umarni kan abin da za a yi idan Iran ta yi nasarar kashe shi.
Shugaba Trump ya bayyana cewa Iran ta dade tana farautar rayuwarsa domin daukar fansa kan abin da ya yi a baya.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar New York Post, inda ya ce Iran ta dade tana sanya shi cikin jerin mutanen da take son kashewa.
Wace wasiyya Trump ya bari?
"Sun dade suna nemana. Wannan shi ne abin da muke fuskanta. Abin da na yi shi ne na bar umarni cewa idan wani abu ya same ni, a kai musu hari mai muni fiye da duk abin da suka taba gani."
- Donald Trump
Trump ya kuma yi barkwanci da cewa:
"Ina fatan za ku yi kewata."
Trump ya ce ba sabon shiri aka gano ba
Da aka tambaye shi kan rahotannin da ke cewa Isra'ila ta sanar da Amurka game da wani sabon shirin Iran na kashe shi, Trump ya ce babu wata sabuwar makarkashiya da aka gano.
Sai dai ya jaddada cewa Iran ta dade tana son kashe shi.
"A'a, a'a. Isra'ila ba ta gano wani sabon abu ba. Na dade ina na farko a jerin mutanen da Iran ke son kashewa," in ji shi.
Dalilin rikicin Trump da Iran
Iran ta fito fili tana neman daukar fansa kan Trump tun shekarar 2020, bayan ya ba da umarnin harin da ya kashe babban kwamandan sojojin Iran, Janar Qasem Soleimani.

Kara karanta wannan
Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo
Tun daga lokacin, dangantakar kasashen biyu ta ci gaba da tsami.

Source: Facebook
Tashin hankali ya sake karuwa
A cikin makon nan, rikicin ya sake daukar sabon salo bayan wasu masu zanga-zanga a wajen jana'izar jagoran Iran sun daga manyan alluna masu kira da a kashe Trump.
Rahotannin kafafen yada labaran Iran sun ce wani mai jawabi a wajen taron jana'izar ya bayyana cewa:
"Me zai hana mu kashe wanda ya kashe limamina da shugabana? Kashe Trump wajibi ne a gare mu. Me ya sa mafi munin mutum a duniya har yanzu yana raye?"
Har ila yau, Trump ya tsallake hare-haren kisan gilla fiye da daya a baya-bayan nan, ciki har da harbin da ya wuce ta gefen kunnensa a wani gangamin yakin neman zabe da aka gudanar a Butler, jihar Pennsylvania, a ranar 13 ga Yulin 2024.
Trump ya sauya jirgi a Turkiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bar kasar Turkiyya a tsohon jirgin saman shugaban kasa a maimakon sabo.
Wasu jami'an gwamnatin Amurka hudu sun nuna cewa an dauki wannan mataki ne saboda damuwar tsaro da ta taso sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Amurka da Iran.
Asali: Legit.ng
