'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci a Zamfara, an Kashe Manoma a Gonakinsu

'Yan Bindiga Sun Sake Ta'addanci a Zamfara, an Kashe Manoma a Gonakinsu

  • 'Yan bindiga sun kashe manoma da dama a kauyen Sauna/Ruwan Gora da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara
  • Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun bude wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta tare da binsu har suka kashe wadanda suka yi kokarin tserewa
  • Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da gwamnatin tarayya da su kara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Talata Mafara, Zamfara - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe manoma a wani hari sa suka kai a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun kashe akalla manoma 23 a kauyen Sauna/Ruwan Gora da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin yankin da ya yi magana da Daily Trust bisa sharadin sakaya sunansa ya ce da farko 'yan bindigan sun ratsa kauyen da misalin karfe 2:00 na rana ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2026 ba tare da sun kai wa kowa hari ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: An yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan sace daliban Oyo

"'Yan bindigan sun ratsa kauyenmu da misalin karfe 2:00 na rana ba tare da sun cutar da kowa ba. Har ma mutane suna kirga yawan babura da suke da su," in ji shi.

Ya bayyana cewa daga bisani maharan sun dawo inda suka bude wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta, tare da bin wadanda suka yi kokarin tserewa.

"Sun kashe mutane 23. Sun kai musu hari a gonakinsu daban-daban, suka bi wadanda suka gudu neman tsira sannan suka kashe su," in ji shi.

Za a binne mutanen da aka kashe

A cewar majiyar, an kammala shirye-shiryen yi wa gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su 23 jana'iza a ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026.

"Mun shirya gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su 23 domin yi musu jana'iza tare a yau," ya kara da cewa.

Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da gwamnatin tarayya da su dauki matakin gaggawa wajen kara karfafa tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyi.

"Idan aka ci gaba da kashe manoma da yin garkuwa da su, babu shakka jihar Zamfara za ta fuskanci karancin abinci," In ji shi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun birkita kauyen Sokoto da harbi, sun sace sama da mutum 50

Adadin wadanda zai iya karuwa

Wani mazaunin yankin, wanda shi ma ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce adadin wadanda aka kashe na iya kai wa 25, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin tantance ainihin adadin wadanda suka rasa rayukansu.

"'Yan bindigar sun dawo suka kai wa kauyen hari da misalin karfe 3:00 na yammacin jiya. Har yanzu muna tattarawa da bin diddigin wadanda suka rasa rayukansu," in ji shi.
'Yan bindiga sun kashe manoma a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ba a samu martani daga hukumomi ba

Kokarin samun martanin hukuma bai yi nasara ba. An kasa samun Shugaban karamar hukumar Talata Mafara, Hon. Yahaya Abubakar Yari, ta wayar tarho, domin wayarsa a kashe take duk da kiran waya da sakonnin WhatsApp da SMS da aka aika masa.

Haka kuma, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, bai amsa kira ko sakonnin waya ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.

'Yan bindiga sun kashe kwamandan 'yan sa-kai

Kara karanta wannan

Babbar magana: An gano jami'ar bogi da ta tara dalibai a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kashe kwamandan 'yan sa-kai na OSPAC na yankin Omoku, Ozomela Stephen Nwaocha a jihar Rivers.

'Yan bindigan sun kuma kashe wasu mata uku a wani hari da suka kai a kan titin Oba Road da ke Omoku, karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni ta jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng