An Kuma Samun Matsala a Shari'ar da Aka Nemi Kwace Kadarorin Malami a Abuja

An Kuma Samun Matsala a Shari'ar da Aka Nemi Kwace Kadarorin Malami a Abuja

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake dage yanke hukunci kan shari'ar kadarorin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami guda 57
  • Rahotanni sun nuna cewa alkalin kotun ba ta samu damar halartar zaman ba, lamarin da ya sa aka ɗage zaman yanke hukunci
  • Hukumar EFCC na neman a kwace kadarorin har abada, yayin da Malami ya ce an mallake su ne ta halastacciyar hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage yanke hukunci kan bukatar kwace kadarori 57 da ake alakantawa da tsohon Ministan Shari'a kuma tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta nemi kwace kadarorin tare da mallakawa gwamnatin tarayya saboda tana zargin an mallake su ta haramtacciyar hanya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke 'yar kasar waje mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

Malami.
Tsohon ministan shari'a kuma tsohon Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami (SAN) a harabar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Yadda alkali ta jawo cikas a kotu

Tashar channels tv ta ruwaito cewa shari'ar, wadda aka tsara za a yanke hukunci a kanta a gaban Mai shari'a Joyce Abdulmalik, ba ta gudana ba saboda alkalin ba ta halarci zaman ba.

Saboda rashin zuwan alƙalin ne, babbar kotun ta sanar da dage yanke hukuncin zuwa ranar 15 ga watan Yulin 2026.

EFCC na son kwace kadarorin Malami

A zaman da ya gabata, lauyan EFCC, Jibrin Okutepa (SAN), ya bukaci kotun ta amince da bukatar hukumar na kwace kadarorin har abada tare da mika su ga gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa bukatar, wadda aka shigar tun watan Fabrairu, 2026, tana goyon bayan rantsuwar shaida mai sakin layi 47 tare da hujjoji 46.

Okutepa ya ce wadanda ake kara, ciki har da Malami, sun gaza bayyana gamsassun hujjojin da ke nuna cewa an mallaki kadarorin ta hanyar da ta dace.

Abun da Abubakar Malami ya fadawa kotu

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

A nasa bangaren, lauyan Malami, Adedayo Adedeji (SAN), ya bukaci kotun ta soke umarnin wucin gadi na kwace kadarorin.

Ya ce Malami ya gabatar da rantsuwar shaida mai sakin layi 109 domin nuna cewa kadarorin ba su fito daga haramtacciyar hanya ba.

Adedeji ya jaddada cewa EFCC ta gina karar ne kan zato kawai ba tare da tabbatattun hujjoji ba, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

"Kotu tana yanke hukunci ne bisa hujjoji, ba zato ba," in ji lauyan Malami.
EFCC.
Babbar hedkwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ke Abuja Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Ya kara da cewa wasu daga cikin kadarorin an mallake su tun kafin Malami ya zama Ministan Shari'a, don haka ba za a iya cewa kudin haram ne aka yi amfani da su wajen sayensu ba.

Haka kuma, ya gabatar da karin rantsuwar shaida a madadin sauran wadanda ake kara da kamfanonin da ke cikin karar, yana mai rokon kotu ta yi watsi da bukatar EFCC ta kwace kadarorin.

Yadda EFCC ta kai samame gidan Malami

An ji cewa hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta kai samame gidan tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami a Maitama, Abuja.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta tura tsohon shugaban CCT ta Najeriya gidan yari a Abuja

An ruwaito cewa jami’an, karkashin jagorancin Folarin Sunday Dare, sun isa gidan da kusan motoci biyar, sanye da rigunan aikinsu, dauke da makamai masu yawa.

Sun kuma rufe hanyar shiga gidan Malami, lamarin da ya hana mutane shiga ko fita, yayin da aka killace yankin baki daya domin gudanar da aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262