'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Tsaro har da Sace Mutane a Abuja
- Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a yankin Mpape da ke Abuja a daren Laraba, 8 ga watan Yulin 2026
- Hatsabiban 'yan bindigan sun kashe jami'in tsaro guda ɗaya, sannan an sace mutum uku ciki har da wani fasto
- Maharan sun tsere bayan sun yi musayar wuta da jami'an tsaro da suka isa wurin domin kai daukin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a wani yanki da ke Mpape a Abuja, inda suka kashe wani jami'in tsaro tare da yin garkuwa da mutum uku, ciki har da wani fasto.
Mpape na da tazarar ƴan mintuna kaɗan da unguwar Maitama da ke Abuja, sannan tana kusa da sansanin sojoji a cikin babban birnin ƙasar.

Source: Original
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa maharan sun isa yankin ne ƴan mintuna kafin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka farmaki wani sabon layi da ake kira Yellow House, suna ƙoƙarin kai hari kan wani gida.
Jami'an tsaro sun dakile farmakin
Wata majiya ta bayyana cewa maharan ba su samu nasarar shiga gidan ba bayan jami'an ƴan sanda da aka sanar da aukuwar lamarin suka isa wurin.
Ta ce nan take aka fara musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da maharan, lamarin da ya tilasta musu janyewa daga yankin.
An sace fasto da wasu mutum biyu
Majiyar ta ƙara da cewa yayin da maharan ke tserewa daga wurin, sun ci karo da wani fasto da ke komawa gidansa, inda suka yi garkuwa da shi.
"Sun yi nasarar sace faston daga cikin motarsa. Haka kuma sun yi garkuwa da wasu mazauna yankin biyu da suka tarar a hanya yayin da suke tserewa." In ji majiyar
An kuma gano motar faston da aka sace a bakin wata hanya da ke cikin unguwar bayan jami'an tsaro sun bi sawunta.

Source: Twitter
An harbi wani mazaunin yankin
Rahotanni sun kuma bayyana cewa wani mazaunin yankin ya samu rauni bayan maharan sun harbe shi a ƙafa yayin harin.
Daga bisani jami'an ƴan sanda sun kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci. Hakazalika, an kuma ji karar harbe-harbe a sassan yankin har zuwa kusan ƙarfe 2:00 na dare.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Babban Birnin Tarayya, SP Josephine Adeh, bai yi nasara ba, domin ba ta amsa kiran waya ko saƙon WhatsApp da aka aika mata ba.
'Yan bindiga sun sace 'yan uwan Dauda Lawal
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayar da labarin yadda 'yan bindiga suka taba sace 'yan uwansa.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ya ƙi biyan Naira miliyan 300 da masu garkuwa da mutane suka buƙata lokacin da suka sace 'yan'uwansa a shekarar 2019.
Yaa ce ya ɗauki wannan matsaya ne saboda ya yi amanna cewa biyan kuɗin fansa yana ƙara ƙarfafa masu aikata laifuka su ci gaba da sace mutane domin neman kuɗi.
Asali: Legit.ng

