Kotu Ta Ɗaure Wani Mutumi a Gidan Kaso bayan Kisan Ƴar Majalisa da Mijinta
- Wata kotun tarayya a Amurka ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin rai da rai a Amurka kan aikata kisan kai
- An daure Vance Boelter sau biyu tare da karin shekara 40 saboda kashe tsohuwar shugabar Majalisar Minnesota Melissa Hortman da mijinta
- Iyalan wadanda abin ya shafa da Sanata John Hoffman sun bayyana irin radadi, tsoro da sauyin rayuwa da suka fuskanta bayan harin da Boelter ya kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minnesota, US - An yanke wa wani dan kasar Amurka, Vance Boelter hukuncin daurin rai da rai sau biyu tare da karin shekara 40.
Hukuncin ya biyo bayan amsa laifin kashe tsohuwar shugabar Majalisar Wakilan Minnesota, Melissa Hortman, da mijinta Mark Hortman.

Source: Twitter
Haka kuma ya harbi Sanata John Hoffman da matarsa Yvette, inda suka samu munanan raunuka, cewar Ma'aikatar Shari'a ta Amurka.
Hukuncin da kotu ta yanke a Amurka
A yayin zaman yanke hukunci, alkalin kotun tarayya John R. Tunheim ya bayyana cewa wannan shi ne hukunci mafi tsauri da ya taba yankewa a cikin dubban shari'o'in da ya saurara.
Sanata John Hoffman ya bayyana wa kotu cewa har yanzu shi da iyalansa na rayuwa cikin tsoro sakamakon harin.
Ya ce sun daina karbar wasiku a gida, sun sanya kofofin karfe masu karfi, kuma sun sauya yadda suke gudanar da rayuwarsu saboda raunukan da suka samu.
Yvette Hoffman ta ce har yanzu tana fama da matsananciyar firgici, kuma tana ganin likitan kwakwalwa duk mako.
Ta ce ba za ta taba mantawa da yadda ta ga jininta yana zuba bayan an harbe ta a gidansu ba.
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa Boelter ya shafe watanni yana bibiyar wadanda ya nufa kafin ya kai harin.
Ya je gidajensu ne da sanyin safiya yana sanye da kayan dan sanda tare da fakewa da cewa yana gudanar da binciken jin dadin mazauna gida.

Source: Getty Images
Yadda wata yar majalisa ta tsira
'Yar majalisar Minnesota Kristin Bahner ta ce ta tsira ne saboda tana hutu tare da iyalanta lokacin da Boelter ya je gidanta.
Ta ce har yanzu tana mamakin dalilin da ya sa ita ta tsira amma Melissa Hortman ta rasa ranta.
'Yan uwan Mark Hortman sun nuna fushinsu kan yadda ba a yanke wa Boelter hukuncin kisa ba.
Sun ce ba su ji dadin cewa zai ci gaba da rayuwa a gidan yari yayin da iyalansu ke fama da bakin cikin rashin masoyansu.
'Ya'yan Melissa da Mark Hortman sun bayyana irin radadin da suke ciki bayan rasa iyayensu.
Sophie Hortman ta tuna yadda suka yi bankwana da karensu Gilbert, wanda shi ma aka harba a lokacin harin.
Colin Hortman ya ce iyayensa ba su halarci bikin aurensa ba saboda an kashe su. Ya ce har yanzu yana fama da tashin hankali, kuka da kuma tuna jinin da ya gani a gidan iyayensa.
Mahaifin Melissa Hortman, Harold Haluptzok, ya ce da maharin ya zauna ya tattauna da 'yarsa kan ra'ayinsa na siyasa da ba a kai ga wannan mummunan lamari ba.
Bayan kashe Melissa da Mark Hortman, Boelter ya kuma fuskanci tuhume-tuhume a kotun jihar, ciki har da kisan kai, yunkurin kisan kai, kwaikwayon jami'in dan sanda da kuma cin zarafin dabba.
Trump ya gindaya sharuda ga Iran
An ji cewa shugaba Donald Trump ya ce yarjejeniyar makamashin nukiliyar Amurka da Saudiyya za ta tabbata ne idan Riyadh ta amince da Isra'ila.
Trump ya jaddada cewa Saudiyya ba za ta riƙa tace sinadarin uranium ba, yana mai cewa shirin ya shafi amfani da makamashin nukiliya.
Saudiyya ta sha bayyana cewa ba za ta amince da Isra'ila ba sai an kafa ƙasar Falasdinu, yayin da Isra'ila ta yaba da sabon sharadin Trump.
Asali: Legit.ng


