An Maka Soja Boy a Kotu kan Bata Sunan Ƴan Jihar Kano da Sunan Luwadi

An Maka Soja Boy a Kotu kan Bata Sunan Ƴan Jihar Kano da Sunan Luwadi

  • Wani dan gwagwarmaya a Kano ya ce ya shigar da ƙara a kotu kan batun da ya shafi mutunci da martabar jihar
  • Mujahid Mohammed Abdullahi ya bayyana cewa Kano jiha ce mai tarihi, addini, ilimi da al'adu, yana gargadin masu kalaman da za su bata sunan jihar
  • Matashin ya shigar da karar game da cin mutuncin jihar da wani mawaki Usman Umar da aka fi sani da Soja Boy ya yi a bidiyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani dan gwagwarmaya a Kano ya shigar da mawaki Usman Umar da aka fi sani da Soja Boy a kotu kan cin mutuncin jihar.

Mujahid Muhammad ya bayyana cewa ya shigar da ƙara a kotu kan batun lamarin da ya shafi mutunci da martabar Jihar Kano, domin kotu ta gudanar da aikinta.

Kara karanta wannan

Ndume ya musanta zargin shiga tsakani da 'yan bindiga, ya nemi a binciki Kaigama

An maka Soja Boy a kotu
Mawaki Usman Umar da aka fi sani da Soja Boy da Mujahid Mohammed Abdullahi. Hoto: Soja Boy, Muhajeed Mohd.
Source: Facebook

Matashin ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 23 ga watan Yulin shekarar 2027.

Abin da ya jawo wa Soja Boy matsala

Hakan ya biyo bayan wani bidiyo da Soja Boy ya yi wanda ya ce ilahirin yan jihar Kano yan luwadi ne.

A cikin ƙarar, mai ƙorafin ya zargi Soja Boy da wallafa wani bidiyo a kafafen sada zumunta inda ya yi iƙirarin cewa babu wata jiha a Nijeriya da ta fi Kano yawan masu luwadi.

Lamarin ya tayar da kura a kafafen sadarwa inda yan jihar da dama suka yi sukarsa ta ko ta ina.

Matashi Mujahid ya ce Kano jiha ce mai tarihi, addini, ilimi da al'adu, wadda ta ƙunshi malamai, sarakuna, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, matasa da sauran al'umma masu mutunci.

Mujahid ya ce bai dace a yi kalaman da za su zubar da martabar ɗaukacin al'ummar Kano ba tare da hujja ba, saboda hakan na iya haddasa rashin fahimta.

Kara karanta wannan

Mai shekara 60 ya rasu bayan zuwa otel da budurwa, an samu maganin jima'i

Ya tabbatar da cewa wannan mataki ya zama gargadi ga duk wanda ke tunanin yin zagon ƙasa ko furta kalaman da za su bata sunan Kano da al'ummarta.

Soja Boy ya shiga matsala kam taba kimar Kano
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Soja Boy: Umarnin kotu ga Kwamishinan yan sanda

Har ila yau, bayan korafin, Babbar Kotun Majistare ta Kano ta umarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano da ya gudanar da bincike kan zarge-zargen da aka shigar a kan Soja Boy.

Wasiƙar da kotun ta aikewa Kwamishinan ’Yan Sandan, mai ɗauke da kwanan watan 21 ga Yuli, 2026, ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan ƙorafin da Mujahid ya shigar, tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannu ko tada tarzoma, su bar kotu ta gudanar da aikinta, yana mai cewa zai mutunta duk hukuncin da kotu za ta yanke.

Soja Boy ya magantu kan korarsa daga Kannywood

A baya, an ji cewa hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da Usman Soja Boy saboda korafe-korafen batsa a bidiyonsa, musamman rungumar mata.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Soja Boy ya bayyana cewa Kannywood ba ta taɓa taimakA masa ba, sai dai shi ne ke taimakon masana’antar ta hanyoyi daban-daban.

Mawakin ya ce dakatarwar ba ta da tasiri a kansa, domin shi ya riga ya samu daukaka da kudi ba tare da taimakon Kannywood ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.