Inganta Tsaro: Gwamnatin Sokoto Ta Dauki 'Yan Marshals Sama da 1,500
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto, ya yaye rukuni na biyu na jami'an Sokoto Marshals guda 1,550 da aka ɗauko daga dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar
- Gwamnan ya ce shirin ba wai samar da aikin yi kawai ba ne, har ila yau wata muhimmiyar dabara ce ta ƙarfafa tsaron al'umma, kare rayuka da dukiyoyi a Sokoto
- Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya yaba da matakin gwamnatin Sokoto, yana mai cewa wani abin koyi ne da sauran jihohin Najeriya za su iya kwaikwaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sokoto – Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto, ya sanar da kammala horaswa tare da yaye rukuni na biyu na jami'an Sokoto Marshals guda 1,550 da aka zaɓo daga dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Ahmad Aliyu ya ce shirin yana nuna jajircewar gwamnati wajen gina jihar Sokoto mai zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce matakin ya zama wani sabon ci gaba a ƙoƙarin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsaro da ci gaba mai ɗorewa a jihar.
Gwamna ya fadi manufar shirin
Ahmad Aliyu ya ce shirin Sokoto Marshals ya wuce batun ɗaukar ma'aikata kawai, domin wata dabarar gwamnati ce ta ƙarfafa matasa, inganta tsaron al'umma da kare rayuka, dukiyoyi da kayayyakin gwamnati.
Ya bayyana cewa sake farfaɗo da rundunar a ƙarƙashin sabuwar doka zai samar wa matasa damar aiki tare da ƙarfafa tsarin tsaron jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Sokoto.
Gwamnan Ekiti ya yabi Sokoto
Ahmad Aliyu ya gode wa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, wanda ya halarci bikin a matsayin babban baƙo na musamman.
Ya ce gwamnan Ekiti ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin Sokoto, yana mai bayyana shirin a matsayin abin koyi da sauran jihohi za su iya kwaikwaya.
Haka kuma ya nuna godiya ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, hukumomin tsaro, masu horas da jami'an da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bai wa shirin.
Gwamna Ahmad Aliyu ya buƙaci sababbin jami'an da aka yaye su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, ƙwarewa, ladabi da bin doka.

Source: Facebook
Ya ce ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
An sace mutane a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace fiye da mutum 50 a ƙauyen Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyen da dare, inda suka yi awon gaba da mata kusan 30 da kuma sama da almajirai da sauran maza 20.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an yi tattaunawa da maharan, inda suka nemi kuɗin fansa kafin su saki waɗanda suka sace daga baya.
Asali: Legit.ng

