Trump Ya Kara Tsaurara Matakan Kasuwanci, Ya Laftawa Najeriya Haraji

Trump Ya Kara Tsaurara Matakan Kasuwanci, Ya Laftawa Najeriya Haraji

  • Amurka ta sanar da kakaba harajin kashi 12.5 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Najeriya saboda zargin rashin dakile kayayyakin da aka samar da aikin tilas
  • Sabon matakin ya shafi kasashe 60, inda Amurka ta ce ba su kafa ko aiwatar da dokokin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole ba
  • Hukumar Kasuwancin Amurka ta ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin Donald Trump na yaki da amfani da aikin tilas a harkokin kasuwanci na duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba sabon harajin kashi 12.5 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Najeriya.

Sabon matakin ya biyo bayan binciken da USTR ya gudanar kan manyan abokan hulɗar kasuwancin ƙasar, inda aka ce Najeriya na cikin ƙasashen da ba su aiwatar da dokokin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani mutumi a gidan kaso bayan kisan ƴar majalisa da mijinta

Bola Tinubu da Donald Trump
Bola Tinubu a hagu da Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa harajin zai shafi kayayyakin Najeriya da ake fitarwa zuwa Amurka, sai dai wasu kayayyaki da aka ware daga cikin tsarin.

Dalilin Amurka na kakaba harajin

A wata sanarwa da USTR ta fitar ta bayyana cewa an gudanar da binciken ne tun watan Mayun 2026 ƙarƙashin sashe na 301 na dokar kasuwanci ta Amurka.

Hukumar ta ce ta karɓi sama da rubuce-rubuce 1,600 daga jama'a, ta saurari shaidu fiye da 100 tare da tuntuɓar gwamnatoci sama da 45 kafin yanke wannan hukunci.

A cewar hukumar, ƙasashen da suka riga suka kafa ko suka yi alkawarin aiwatar da dokokin hana kayayyakin da aka samar da aikin tilas za su fuskanci harajin kashi 10 cikin 100 kacal.

Sai dai Najeriya na cikin ƙasashen da za su biya harajin kashi 12.5 cikin 100 saboda abin da hukumar ta bayyana a matsayin gazawa wajen aiwatar da irin waɗannan matakai.

Abin da USTR ta ce kan Najeriya

Kara karanta wannan

Trump ya lallaba ya tura bukatar tsagaita wuta Iran ta Iraq, Tehran ta yi martani

A cikin takardar sanarwar da aka fitar, USTR ta ce za a kakaba harajin kashi 12.5 cikin 100 kan kayayyakin Najeriya, ban da wasu kayayyakin da aka ware daga tsarin.

Leadership ta rahoto cewa hukumar ta ce an yanke hukuncin ne bayan nazarin bayanan da aka tattara, shawarwarin kwamitocin da abin ya shafa da kuma umarnin shugaban ƙasa Donald Trump.

Ta kuma bayyana cewa wasu kayayyaki za su ci gaba da samun rangwame, musamman waɗanda rashin shigo da su zai iya janyo ƙarancin albarkatun ƙasa ko matsala ga tattalin arzikin Amurka.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Rahoton ya nuna cewa sabon harajin ya zo ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da sashe na 122 na dokar kasuwanci ta shekarar 1974 domin ƙaddamar da wasu sabbin matakan haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar.

Amurka ta yi korafi kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da kisan wasu 'yan uwan Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Filato.

Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya bayyana harin a matsayin abin takaici, tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan mamatan da sauran waɗanda lamarin ya shafa.

Har ila yau, gwamnatin Amurka ta buƙaci hukumomin tsaro su kamo masu hannu a harin tare da ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng