"Ba Kushe ba": Shugaban APC, Nentawe Ya ba 'Yan Adawa Shawara ana Shirin Zaben 2027

"Ba Kushe ba": Shugaban APC, Nentawe Ya ba 'Yan Adawa Shawara ana Shirin Zaben 2027

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bukaci 'yan adawa su daina sukar gwamnati kawai
  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce ya kamata 'yan siyasa su gabatar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin Najeriya
  • Yilwatda ya ce cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewar kasafin kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bukaci shugabannin 'yan adawa su daina sukar gwamnati kawai.

Farfesa Nentawe ya bukaci su mayar da hankali wajen gabatar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin Najeriya.

Nentawe ya ba 'yan adawa shawara
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Yilwatda ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yada labarai da dabarun yada bayanai, Abimbola Tooki, ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

PFIPC: Atiku ya ba majalisa mafita bayan CBN da Akanta janar sun yi baki 2

An fitar da sanarwar ne bayan kammala bikin cin abincin dare na bayar da lambobin yabo ga Majalisar Dokoki ta Kasa karo na 10 da aka gudanar a Abuja.

Da yake magana ta bakin wakilinsa, Daniel Rejenieju, shugaban APC na kasa ya bukaci 'yan siyasar adawa su daina yin Allah wadai da manufofin gwamnati kawai, su kuma bayar da gudunmawa mai ma'ana wajen ci gaban kasa.

Dalilin cire tallafin man fetur

Ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta yi, mataki ne da babu makawa kuma ya zama dole domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durkushewar kasafin kudi da ke gabatowa.

Shugaban jam'iyyar na kasa ya bayyana tsarin tallafin da ake yi a baya a matsayin wanda ba zai dore ba, yana mai cewa ya amfanar da wasu tsirarun masu gata ne kawai, yayin da ya hana kasar kudaden da take bukata domin muhimman ayyukan ci gaba.

Ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da nuna goyon baya ga sauye-sauyen tattalin arziki masu muhimmanci da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya sake huro wuta sai Tinubu ya yi murabus

Nentawe ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya

Farfesa Yilwatda ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa wahalhalun da ake fuskanta na dan lokaci sakamakon sauye-sauyen za su kawo karshen su, tare da samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa, daidaiton kasafin kudi da kuma wadata da za ta amfanar da kasa baki daya.

"Kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a yanzu sakamako ne na dan lokaci na sauye-sauyen da aka tsara domin gyara matsalolin tsarin da suka dade suna addabar kasa," in ji Yilwatda

Ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya nuna kudurin kawo gyara da gwamnatocin da suka gabata suka kasa nunawa, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Nentawe ya shawarci 'yan adawa
Farfesa Nentawe Yikwatda na jawabi a wajen taron APC Hoto: @nentawe1
Source: Facebook

Shugaban APC ya gana da Kabiru Gaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar girmamawa ga jigon jam'iyyar NDC a Kano, Sanata Kabiru Gaya.

Farfesa Nenatwr Yilwatda ya bayyana cewa tattaunawar da suka yi ta fi mayar da hankali ne kan haɗin kan al'ummar Kano da kuma buƙatar shugabanni su ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng