Obasanjo Ya Tsame Kansa kan Zargin Kifar da Tsohon Gwamna, Ya Saka Sunan Atiku

Obasanjo Ya Tsame Kansa kan Zargin Kifar da Tsohon Gwamna, Ya Saka Sunan Atiku

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi karin haske kan zargin kayar da tsohon gwamna a 2003
  • Obasanjo ya zargi tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar da shirya yunkurin tsige shi tare da yin aiki domin hana sake zabensa a 2003
  • Ya ce siyasa ba ta kamata ta lalata dangantaka ba, yana mai jaddada cewa hadin kan kasa ya fi siyasar kabilanci muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana gaskiya kan zarginsa a zaben shekarar 2003.

Obasanjo ya yi watsi da ikirarin tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba, cewa ya yaudari shugabannin jam'iyyar AD kafin zaben shekarar 2003.

Obasanjo ya zargi Atiku da shirin tsige gwamna a 2003
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo. Hoto: @atiku.
Source: Twitter

Hakan na cikin martaninsa mai taken "Reply to Your Inaccurate Posture: 'How Obasanjo Deceived Us in 2003'", cewar Punch.

Obasanjo ya kare kansa kan zargin tsohon gwamna

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Ya bayyana zargin a matsayin marar tushe kuma mai cike da kuskure, inda ya ce bai taba yaudarar kowa ba, ya ce kullum yana bayyana matsayinsa da gaskiya ba tare da boye wani abu ba.

Ya ce Osoba bai san wasu muhimman tattaunawar siyasa da suka gudana tsakaninsa da shugabannin Afenifere da AD ba, domin manyan dattawan kungiyar ne suka jagoranci wadannan shawarwari.

Obasanjo ya kare sakamakon zaben gwamnoni na Kudu maso Yamma a 2003, inda PDP ta lashe jihohi biyar daga cikin shida.

Sai dai ya yi ikirarin cewa a wata jiha daya an sauya sakamakon zabe ba bisa ka'ida ba, ya kuma ce Osoba bai gudanar da yakin neman zabe sosai ba, har ya nemi afuwar jama'ar Ogun a wani shirin talabijin.

Zargin da Obasanjo ke yi wa Atiku

Tsohon shugaban kasar ya kuma zargi tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar da shirya yunkurin tsige shi ta hannun marigayi kakakin majalisar wakilai, Ghali Na'Abba.

A cewarsa, Atiku ya gayyaci Na'Abba zuwa ofishinsa yayin da yake wajen aiki, sannan ya ba shi Naira miliyan biyar domin fara shirin tsige shi.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Obasanjo ya ce jami'in leken asirin da ke shugabancin ma'aikatansa ne ya sanar da shi hakan, cewar TheCable.

Ya kara da cewa bayan shirin tsige shi ya gaza, Atiku ya sake kokarin kulla yarjejeniya da gwamnonin AD shida domin su mara masa baya a zaben shekarar 2007.

Obasanjo ya ce an yaudari gwamnonin AD da cewa shi ne ke goyon bayan wannan shiri, alhali bai taba amincewa da irin wannan tsari ba.

Obasanjo ya saka sunan Atiku kan zargin shirya tsige tsohon gwamna
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: @atiku.
Source: Twitter

Obasanjo ya tuna mulkinsa a 1999

Tsohon shugaban kasar ya kare matakin da ya dauka na bai wa wasu 'yan AD mukamai a gwamnatinsa bayan ya hau mulki a 1999, yana mai cewa manufarsa ita ce hada kan kasa, ba rauni ba.

Ya ce bai yarda gwamnoni shida na adawa za su iya rinjayar shugaban kasa ba, musamman ganin yana da goyon bayan gwamnoni talatin, majalisar dokoki da majalisar zartarwa.

Duk da sabanin siyasar da suka yi, Obasanjo ya yabawa Osoba saboda ware filin da aka gina dakin karatun Olusegun Obasanjo a Abeokuta, yana mai cewa wannan na daga cikin manyan gudummawar da ya bayar ga Ogun.

Kara karanta wannan

'Mun daina bautawa siyasa', Fahad Dankabo ya kawo sabon salo a siyasar Kano

Obasanjo ya magantu kan sake yakin basasa

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi gargadi cewa Najeriya ba za ta iya fuskantar wani yaƙin basasa na biyu ba bayan wanda aka yi a baya.

Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu ba a magance wasu daga cikin matsalolin da suka haifar da yaƙin basasa daga 1967 zuwa 1970 a Najeriya ba.

Haka zalika ya yabawa waɗanda suka tattara tarihin kisan gillar Asaba, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen hana sake faruwar irin haka a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.