Latest
Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci Musulmin Najeriya su fita neman jinjirin watan Rabi’ul Sani na shekarar 1448H ranar Juma’a, 11 ga Satumba 2026.
Ƙungiyar Charismatic Bishops Conference of Nigeria ta ayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu domin sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Matar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Titi Abubakar, ta ce a zaɓi mijinta a zaɓen 2027, ta ce ayyukansa masu kyau za su sa mutane da kansu su buƙaci ya maimaita.
Kasar Amurka ta bai wa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya kayan aikin soja domin taimakawa ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci a musamman Arewacin Najeriya.
Dan takarar shugaban kas a SDP, Adewole Adebayo ya ce zai iya nada Nyesom Wike minista idan ya zama shugaban Najeriya, amma zai takaita kalamansa a bainar jama’a.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce shirin NELFUND ya taimaka wajen rage wa yaran talakawa matsalar kuɗin karatu a manyan makarantu.
Shugaba Donald Trump, ya yi hasashe yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da kasar musulunci ta Iran zai ƙare bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka na watan Nuwamba, 2026.
APC na fuskantar sabon rikici a Bauchi bayan wasu yan takarar majalisar dokokin jihar sun zargi jam’iyyar da sauya sunayensu bayan sun yi nasara a zaɓen fidda gwani.
Kwastam ta kwace bindigogi 204 da aka boye cikin kwantena a Tin Can Port, Legas, tare da gano sassan makamai da aka yi yunkurin shigowa da su Najeriya.
Masu zafi
Samu kari