"Allah ne Ya Cece Ni," Gwamna Ya ba da Labarin Yadda Aka Yi Yunkurin Kashe Shi a Gidansa

"Allah ne Ya Cece Ni," Gwamna Ya ba da Labarin Yadda Aka Yi Yunkurin Kashe Shi a Gidansa

  • Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya bayyana yadda ya tsira daga wani hari da ya kira yunƙurin kashe shi a 2015
  • Alex Otti ya ce ya bar Abuja a lokacin kafin maharan su kai hari gidansa, inda suka kashe ’yan sanda biyu
  • Gwamnan ya ce imaninsa ga Ubangiji ne babban abin da ya ba shi ƙarfin gwiwar fuskantar duk wani ƙalubalen siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya ba da cikakken bayani kan yadda ya shiga siyasa, inda ya ce shawarar da ya yanke ta bauta wa Allah ce ta taimaka masa ya tsallake wasu ƙalubalen siyasa da suka yi barazana ga rayuwarsa.

Gwamna Otti ya bayyana hakan ne a daren Alhamis yayin taron “Abia Solemn Assembly and Covenant Renewal Service” da gwamnatin jihar ta shirya a Umuahia.

Kara karanta wannan

An hada mata musulmai da Allah SWT kan sake zaben Tinubu da Shettima a 2027

Gwamna Otti.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti a gidan gwamnatinsa da ke Ummuahia Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

A rahoton Vanguard, gwamnan ya ba da cikakken labarin wani mummunan hari da ya bayyana a matsayin “yunƙurin kisan gilla” da aka yi masa.

Gwamna Otti ya tuna abin da ya faru

Otti ya ce wani abokinsa ya tuna masa da wasu abubuwan da suka faru a lokacin da ya shiga siyasa, musamman wani lamari da ya faru a watan Yulin 2015 wanda, a cewarsa, saura kiris ya rasa ransa.

Ya tuna cewa ya tsaya takarar gwamnan Abia a zaɓen 2015, sannan ya garzaya kotun sauraron ƙararrakin zaɓe domin ƙalubalantar sakamakon da ya ba ɗan takarar gwamnan PDP, Okezie Ikpeazu, nasara.

Ya ce a lokacin yana Abuja yana ƙoƙarin ganawa da wani mutum, amma mutumin ya ci gaba da sauya ranakun ganawar har ta kai ga ba a yi taron ba.

Yadda aka kusa kashe Alex Otti

Gwamna Alex Otti ya ce daga bisani ya sanar da abokansa cewa zai bar Abuja washegari saboda ba yi ganawar ba, duk da cewa abokansa sun yi masa ƙorafi.

Kara karanta wannan

El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare

“Jirgi ɗaya ne kawai yake tashi daga Abuja zuwa Owerri a lokacin. Dukkan abokaina sun ƙi amincewa. Na ce, to, na samu saƙon cewa dole in bar Abuja.
“Don su fahimta, sai na gaya musu cewa ina son kasancewa a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ranar Juma’a, don haka suka amince da ƙyar.
“A wannan daren, wasu miyagu suka kai hari gidana da ke Abuja, suka harbe ’yan sanda biyu har lahira, kuma suka nemi inda nake amma Allah ya riga ya fitar da ni daga wurin."

- Gwamna Alex Otti.

Alex Otti.
Gwamnan jihar Abia, Alex Itti yana magana a wurin taro a fadar gwamnati Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Otti ya ce bayan maharan sun kasa ganinsa, ya fahimci suna zaton har yanzu yana cikin unguwar, don haka suka shiga harabar gidan da ke makwabtaka da shi domin ci gaba da bincike, cewar Premium Times.

Da yake tunawa da lamarin, Otti ya ce babu wani dalili bayyananne da ya sa zai bar Abuja a wannan lokacin, amma ya yi imanin cewa Allah ne ya shiryar da shi ya tafi.

Gwamna Otti na fatan tazarce a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Alex Otti ya bayyana kwarin gwiwarsa na sake lashe zaben Sbia, yana mai cewa zaben shekarar 2027 zai fi masa sauki idan aka kwatanta da na baya.

Gwamna Otti ya ce ba ya jin tsoron zaben 2027, domin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawansa mulki za su taimaka masa matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262