Matar Atiku Ta Shigo Fage, Titi Ta Yi Magana game da Mulkin Shugaba Tinubu
- Duk da Atiku ya yi alkawarin yin zango ɗaya kacal, Titi Abubakar ta fara kawo masa zancen yin shekaru takwas a ofis
- Ta ce 'yan Najeriya za su roƙe shi ya cigaba da mulki ba don komai ba sai don irin nasarorin da zai samu a gwamnati
- Misis Titi ta soki gwamnatin Tinubu Bola, ta ce komi ya lalace a ƙasar har ta kai ba a amfani da wani kasafin kudi a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Titi Atiku Abubakar ta yi kira ga matasa da su zabi Mai gidanta wato ‘dan takaran ADC ya zama shugaban kasa.
Titi Atiku Abubakar ta na so a ba shi goyon baya ya koma Aso Rock, ta ce idan ya samu mulki, to san an yi burin ya zarce.

Source: Facebook
Titi Abubakar ta hadu da magoya bayan ADC
Matar ta yi wanan kira ne wajen wani zama da aka yi a Abuja da kungiyoyin da ke goyon bayan ADC a cewar The Cable.
Yayin da aka buga gangar kamfe, Titi ta yi kira da babbar murya ga matasa da su shiga harkar siyasar nan a dama da su.
Duk da Atiku ya yi alkawarin zai yi shekaru hudu ne kawai a ofis, mai dakinsa ta ce mutane za su nemi ya cika wa’adinsa.
Zaben 2027 ya fito da Titi Abubakar
Kusan tun da aka fara yakin neman zabe, Titi tana cikin matan ‘yan takaran da aka ji sun fito suna neman kuri’un al’umma.
Ita Titi ta shaida wa magoya baya cewa da yardar Ubangiji idan Atiku ya hau karaga, sai an rika fatan ya zarce a karagar mulki.
Har an fara zancen magajin Atiku
A wa’adin farko, uwargidar ta ce Atiku zai horar da mataimakinsa ta yadda zai gaje shi a lokacin da shi zai bar fadar Aso Rock.
“Zuwa lokacin ya horar da mataimakinsa, watakila mataimakin zai karbi mulki daga hannunsa.”

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya sa Majalisar kolin harkokin Musulunci ta dauki zafi a shari’ar El Rufai
- Titi Abubakar
Gwamnatin Tinubu ta sha bulaliyar matar Atiku
Da ta ke zancen mulkin Tinubu kuwa, ta ce abubuwan sun lalace ta kai babu wani abin da yake daidai karkashin gwamnatin APC.
Daily Trust ta ce Titi ta na mai mamakin yadda talakawa suke iya cin abinci ganin halin da aka shiga da shugaba Tinubu ya karbi iko.

Source: Getty Images
Ta ce:
“Tun daga 2023 har zuwa yau, babu wani kasafin kudi a Najeriya. Ina mamakin yadda ake rayuwa. Ina mamakin yadda mitane suke cin abinci.”
Ta ce ba su da kudin da za su raba amma da zarar an zabi ADC, matar ta ce labarin zai canza domin Wazirin Adamawa zai gyara al’amura.
Remi Tinubu ta ce a zabi mijinta a 2027
A makon nan, an ji Remi Tinubu ta yi makamancin wannan kira ga jama’a, ta roki su zabi mai gidanta ya kara shekaru hudu.
Sanata Remi ta tallata shugaban kasar ne lokacin rabon tallafi da aka yi a jihar Imo, tana neman kuri’un matan kabilar Ibo.
Uwargidar Najeriyar ta ce mai gidanta da gaske yake yi wajen gyara kasa kuma tana fatan ta shana lokacin shekarun sun ja.
Asali: Legit.ng

