‘Zan ba Shi Mukami Bisa Sharadi’: Dan Takarar Shugaban Kasa game da Fitinar Wike

‘Zan ba Shi Mukami Bisa Sharadi’: Dan Takarar Shugaban Kasa game da Fitinar Wike

  • Dan takarar SDP, Adewole Adebayo, ya ce zai iya nada Nyesom Wike minista idan ya zama shugaban Najeriya, amma zai takaita kalaman jama’a na ministan
  • Adebayo ya yaba da kwazon Wike wajen ayyukan raya Abuja, yana cewa ayyukan more rayuwa da yake jagoranta sun saukaka zirga-zirga
  • Duk da yaba masa, Adebayo ya soki salon siyasar Wike da yadda yake bayyana ra’ayoyinsa, yana cewa zai “liƙa tef a bakinsa” idan ya nada shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ce zai nada Ministan Abuja, Nyesom Wike, a gwamnatinsa idan ya zama shugaban Najeriya.

Sai dai Adebayo ya ce zai takaita yadda Wike zai rika yin kalamai a bainar jama’a, duk da cewa yana yaba wa ministan saboda kwazonsa wajen aiki.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027, Gwamna Abba ya aika saƙo ga 'Kwankwaso' da 'yan siyasa a Kano

Adebayo zai iya ba Wike mukami
Dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo da Nyesom Wike. Hoto: Prince Adewole Adebayo.
Source: Facebook

Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da Symfoni, inda ya yi magana kan shugabanci, ayyukan gwamnatin Bola Tinubu da kuma wasu sabbin al’amuran siyasa.

Ya ce yana mutunta Wike saboda jajircewarsa wajen aiki, musamman yadda yake jagorantar ayyukan raya Abuja tun bayan da aka nada shi ministan babban birnin.

Adebayo ya ce irin ayyukan da ake gudanarwa a Abuja karkashin jagorancin Wike sun fi na wasu ministocin da suka gabace shi tasiri.

Ya ce da kwamishinonin ayyuka a jihohin Najeriya za su nuna irin wannan jajircewa, hakan zai taimaka wajen bunkasa ababen more rayuwa a fadin kasar.

Sai dai dan takarar SDP ya nuna damuwa kan tsadar wasu ayyukan da ake gudanarwa karkashin Wike, yana cewa akwai bukatar duba farashin kwangiloli da amfanin da ake samu.

Duk da haka, ya amince cewa ana aiwatar da ayyukan raya Abuja, kuma mazauna babban birnin suna iya ganin sauye-sauyen da ayyukan suka kawo.

Kara karanta wannan

Ba maganar gyaran lantarki, dan takarar shugaban kasa zai saka wa kowa 'solar'

Adebayo ya ce a matsayinsa na mazaunin Abuja, zirga-zirga ta fi masa sauki sakamakon ayyukan da ake gudanarwa a sassan babban birnin kasar.

Sai dai ya soki salon Wike na sadarwa da jama’a da kuma yadda yake tafiyar da wasu batutuwan da suka shafi amfani da karfin iko.

Ya ce irin wannan salo na iya aika wa matasan Najeriya sakon da bai dace ba game da yadda ya kamata a tafiyar da sabanin siyasa a dimokuraɗiyya.

A cewarsa, bai kamata a rika bai wa ministan damar yin dogon bayani kan batutuwan da suka wuce iyakar aikinsa ba, domin hakan na iya rage martabar mukaminsa.

Adebayo ya ce Wike ya kamata ya fi mayar da hankali kan ayyukansa a Abuja, sannan idan akwai bukatar nuna goyon baya ga shugaban kasa, ya yi hakan a sirrance.

Dan takarar SDP ya ce zai yi la’akari da nada Wike minista saboda iya aiki da kwazonsa, amma zai yi kokarin takaita kalamansa a bainar jama’a.

Ya ce:

“Da a ce ina da tawa gwamnati, zan iya nada Wike, amma zan liƙa masa dan karamin tef a bakinsa.”

Kara karanta wannan

Da gaske Akpabio ya yi wa 'yan Arewa barazanar shan azaba idan Tinubu ya fadi a 2027?

Adebayo ya kuma bayyana Wike a matsayin “minista na daya mafi kwazo” a gwamnatin Tinubu, yana danganta hakan da saurin ayyukan raya ababen more rayuwa a Abuja.

Alkawarin Adebayo ga yan Najeriya

An ji cewa dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin samar da wutar hasken rana ga kowane gida cikin watanni 11.

Adebayo ya ce gwamnatinsa za ta gina masana’antun kera bangarorin hasken rana, tare da horar da ’yan Najeriya aikin.

Dan takarar SDP ya ce tarukan hasken rana za su samar da wutar bukatun gidaje, ayyukan yi da kuma samar da megawatt 32,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.