Abubuwan da Shettima Ya Fada kan Najeriya a Taron Majalisar Dinkin Duniya
- Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bukaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya
- Tinubu ya kuma bukaci a bai wa Afirka kujeru biyar na wucin gadi a majalisar, yana mai cewa tsarin da ake da shi na bukatar gyara
- Shugaban ya bayyana bukatar ne a yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya, inda Kashim Shettima ya wakilce shi a taron karo na 81
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
New York – Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bukaci a yi garambawul ga Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya nemi a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin tare da ikon amfani da kujerar naki.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabinsa ga babban taron zaman tattaunawar Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a birnin New York, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gabatar a madadinsa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ana zargin 'tsoro' ya hana Shugaba Tinubu zuwa taron UNGA a ƙasar Amurka

Source: Facebook
Kashim Shettima ya wallafa hotuna da wasu bayanai game da taron a wani sako da ya fitar a shafinsa na Facebook.
Bukatun da Tinubu ya mika
Shugaban kasar ya ce ya kamata sauya tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya ya fara daga sake fasalin Majalisar Tsaro, domin tsarin da aka kafa a shekarar 1945 bai sake dacewa da yadda ƙarfin duniya yake a shekarar 2026 ba.
Ya ce Najeriya na bukatar, bisa yarjejeniyar Ezulwini da Sanarwar Sirte, a bai wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin tare da dukkan hakkoki da nauyin da ke tattare da kasancewa mamba na dindindin.
Tinubu ya kuma bukaci a bai wa Afirka kujeru biyar na wucin gadi a Majalisar Tsaro.
Ya ce Afirka ba za ta iya ci gaba da ba da gudummawa ga ajandar Majalisar Tsaro ba yayin da ba ta da wakilcin dindindin a cikinta.
Najeriya ta shirya kara taka rawa
Tinubu ya ce Najeriya a shirye take ta kara daukar nauyi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Ya kawo misalin rawar da Najeriya ta taka wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya da shiga tsakani a Laberiya, Saliyo, Darfur, Mali da Gambia.
Shugaban ya ce Najeriya na ci gaba da tallafa wa kokarin shiga tsakani, shugabanci na dimokuradiyya, yaki da ta’addanci da tsaron teku ta hannun ECOWAS, Tarayyar Afirka da sauran kawancen kasashen yankin Gulf na Guinea.

Source: Facebook
Magana kan sauyin yanayi
Tinubu ya yi watsi da abin da ya kira kokarin nuna cewa akwai zabin ci gaba ko kuma kare muhalli, yana mai cewa kasashe masu tasowa na bukatar tallafi domin bunkasa masana’antu tare da rage hayakin da suke fitarwa.
Ya ce kasashe masu tasowa na bukatar fasahar zamani, horo da kudi yaki da sauyin yanayi domin bunkasa tattalin arzikinsu da fadada samar da makamashi.
Shugaban ya ce Afirka na fitar da kasa da kashi 4 cikin 100 na hayakin da ke haddasa dumamar yanayi, amma nahiyar na fuskantar illolin sauyin yanayi fiye da yadda gudummawarta ke nufi.
Ya ce Najeriya ta ci gaba da bin yarjejeniyar Paris tare da aiwatar da tsarin sauya makamashi da zai dace da yanayin kasar.
Magantu kan fasahar AI
Tinubu ya kuma yi kira da a yi amfani da fasahar basirar wucin gadi cikin tsari da kulawa, yana mai cewa fasahar na iya amfani wajen lalatawa ko kuma inganta rayuwar mutane.
Ya ce Najeriya ba za ta bari tsoron fasahar zamani ya hana ta cin gajiyar damar da take samarwa ba.
Shugaban ya ce Najeriya na zuba jari wajen samar da abubuwan more rayuwa na zamani, bunkasa intanet, cibiyoyin kirkire-kirkire, cibiyoyin bincike da kasuwancin fasaha.
Ya gayyaci kasashen duniya da su hada kai da matasan Najeriya wajen amfani da basirar wucin gadi domin ci gaban bil’adama maimakon lalata ta.
Magana kan yaki da ta’addanci
Tinubu ya ce kwarewar Najeriya wajen yaki da 'yan ta'adda da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai ta nuna cewa samun nasarar soja kadai ba zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ba.
Ya ce dole ne a hada nasarar yaki da ta’addanci da ilimi, damar samun aikin yi, shugabanci mai bin doka da kare hakkin jama’a.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Shugaba Tinubu da Kashim Shettima sun karya dokar Najeriya a lokaci 1
Shugaban ya ce ci gaba ba zai samu gindin zama ba a wuraren da tashin hankali ke ci gaba da rusa hanyoyin samun abin dogaro da kai.
Kiran Sultan ga Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar JNI), karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta bukaci gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ta gaggauta kawo karshen zubar da jini a Najeriya.
Babban sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya ce Sultan ya yi addu’ar Allah Ya dawo da zaman lafiya a Arewa da Najeriya baki daya, yayin da kungiyar ta bukaci a sake duba tsarin tsaron kasar.
JNI ta ce hukumomin tsaro ya kamata su kara mayar da hankali kan amfani da bayanan sirri wajen dakile hare-hare kafin su faru, tare da ganowa da tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
Asali: Legit.ng

