Shettima Ya Bayyana Shirin Gwamnatin Tinubu da Ya Taimaki 'Ya'Yan Talakawa

Shettima Ya Bayyana Shirin Gwamnatin Tinubu da Ya Taimaki 'Ya'Yan Talakawa

  • Kashim Shettima ya bayyana NELFUND a matsayin wani muhimmin shiri da ke taimaka wa yaran talakawa wajen samun damar yin karatun gaba da sakandare
  • Ya ce shirin yana biyan kuɗin makaranta tare da ba ɗalibai tallafin kuɗin kula da kansu a kowane wata
  • Shettima ya ce Najeriya na kan hanyar samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa, yana danganta hakan da wasu sauye-sauyen tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) a matsayin wani muhimmin shiri da ya taimaka wa yaran talakawa wajen samun tallafin kuɗin karatu.

Shettima ya ce Gwamnatin Tarayya ta mayar da NELFUND wani muhimmin shiri wajen rage gibin tattalin arziki da kuma yaɗa damar samun ilimi a Najeriya.

Kashim Shettima ya yabi NELFUND
Kashim Shettima zaune a ofis Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

NELFUND ya taimaka wa 'ya'yan talakawa

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026 a Abuja.

Shettima ya yi magana ne yayin da ya karɓi tawagar shugabannin Jami’ar Abuja, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jami’ar, Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi.

Ya ce tsarin NELFUND na biyan kuɗin makaranta da kuma samar da tallafin kuɗin kula da kai a kowane wata ya taimaka wajen rage matsalar kuɗi da ke hana ɗalibai zuwa manyan makarantu.

A cewarsa, talauci bai kamata ya zama dalilin da zai hana ɗalibi samun damar ci gaba da karatu ba.

Shettima ya ce tattalin arziki na samun ci gaba

Shettima ya kuma ce Najeriya na kan hanyar samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya danganta wannan ci gaba da ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen waje, ƙarin yawan man fetur da ake samarwa da kuma karuwar rabon kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bai wa jihohi, The Punch ta kawo labarin.

Ya yabawa shugabancin Jami’ar Abuja

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya kamata ya sa 'yan Arewa su ki zabar Tinubu a 2027'

Mataimakin shugaban ƙasar ya yaba wa shugabancin Jami’ar Abuja ƙarƙashin Farfesa Fawehinmi, yana mai cewa ya samar da jagorancin da ya taimaka wajen shawo kan ƙalubalen da jami’ar ta fuskanta a baya.

Shettima ya ce yanzu Jami’ar Abuja ta samu ingantaccen tushe, yayin da aka dawo da cikakken kwanciyar hankali a cikin jami’ar.

Ya kuma yi alƙawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi duk abin da za ta iya domin bai wa jami’ar tallafin da take buƙata.

Shugaban jami’ar ya yaba da NELFUND

Tun da farko, Farfesa Fawehinmi ya ce NELFUND ya taimaka matuƙa wajen samar da ɗan kwanciyar hankali a fannin ilimi a Najeriya.

Ya ce shirin ya taimaka wa ɗalibai wajen samun damar ci gaba da zama a makaranta da kuma kammala karatunsu ba tare da fuskantar matsalar kuɗi mai tsanani ba.

Shettima ya ce NELFUND ya taimaka
Kashim Shettima na addu'a a wajen taro Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Tinubu ya yabi Kashim Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya mataimakinsa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa a duniya.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana mataimakin shugaban kasar a matsayin ɗan kishin ƙasa kuma abokin hulɗa amintacce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng