Gwamna Ya Hango Matsala, Ya Dakatar da Sarki daga Mulki a Najeriya
- Gwamnatin Jihar Enugu karkashin jagorancin Gwmana Peter Mbsh ta dakatar da Sarkin gargajiya na Ibagwa Opi Ogbozalla kan zargin rashin da’a
- Ana zargin basaraken da kin bin dokar gudanar da shugabancin al’umma da kuma kasa kafa majalisar masarauta
- Rahotanni sun nuna cewa matakin dakatarwar ya fara aiki nan take, a cewar Kwamishinan Harkokin Sarautun Gargajiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu, Nigeria - Gwamnatin Jihar Enugu ta dakatar da Williams Ezugwu, Sarkin gargajiya na Ibagwa Opi Ogbozalla da ke ƙaramar hukumar Nsukka, kan zargin rashin da’a.
Kwamishinan Harkokin masarautun gargajiya na jihar Enugu, Charles Egumgbe, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis, 24 ga watan Satumba 2026.

Source: Twitter
Yadda aka dakatar da wasu sarakuna
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa jami’in Hulɗa da jama’a na ma’aikatar harkokin masarautu ta jihar Enugu, Emeka Nebeife, ne ya rattaba hannu a sanarwar da aka fitar a Enugu a madadin kwamishina.

Kara karanta wannan
Atiku ya ziyarci Neja, ya bayar da tallafi ga iyalan mutanen da suka mutu a hannun NSCDC
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tuna cewa gwamnatin jihar ta Enugu ta dakatar da sarakunan gargajiya uku da shugabannin ƙungiyoyin jama’a huɗu a baya.
An dakatar da wadannan shugabannin al'umma ne a yankin ƙaramar hukumar Ezeagu a watan Yuli kan zargin rashin da’a da ya shafi harkokin tsaro.
Me yasa aka dakatar da Sarkin?
Mista Egumgbe ya ce an dakatar da basaraken ne saboda zargin “ci gaba da aikata abubuwan da ba su dace da wasu sassa na Dokar Sarautun Gargajiya ta Jihar Enugu ba.”
A cewar sanarwar, dakatarwar ta fara aiki nan take daga ranar da aka fitar da sanarwar gwamnati a hukumance.
Daga cikin zarge-zargen da ake yi wa basaraken akwai rashin amincewa da bin dokar ɗabi’a da al’ummar yankin ta tanada domin gudanar da harkokin jagorancin al'umma.
Ana kuma zarginsa da kin kafa majalisar sarakuna da ke karkashin masarautarss, wacce da za ta taimaka wajen tafiyar da harkokin al’umma tun bayan ƙirƙirar yankin.

Source: Original
Haka kuma, ana zarginsa da kasa kafa kwamitin gudanarwa na ƙungiyar haɗin kan al’umma, lamarin da ya sa ake cewa yana tafiyar da harkokin al’ummar shi kaɗai ba tare da sauran mataimaks ba.
Kwamishinan Enugu ya ce ayyukan basarake na iya jefa al’ummar da yake jagoranta cikin rikicin da za a iya kauce masa, shi ya sa aka dakatar da shi nan take.
Gwamna Mbah ya nada sababbin hadimai
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya amince da naɗin sababbin hadimai 101 da suka haɗa da masu ba shi shawara da manyan mataimaka na musamman.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Farfesa Chidiebere Onyia, ya fitar ranar Litinin, inda ya ce naɗin ya fara aiki nan take.
A cewar Onyia, mutum bakwai daga cikin waɗanda aka naɗa masu ba da shawara na musamman ne, shida manyan mataimaka na musamman, yayin da 88 kuma mataimaka na musamman ne.
Asali: Legit.ng
