Kaico: Abin da Ya Faru Wanda Ya Kai ga Kashe Babban Malamin Jami'ar ABU, Ya ba da Wasiyya
- Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Dr Iliyasu Abubakar Sadiq daga gidan gonarsa da ke kusa da Jami’ar ABU Zaria daga bisani suka kashe shi
- Rahotanni sun nuna cewa malamin ya roƙi matarsa Baraka da ta kula da ’ya’yansu yayin da ’yan bindigar suka tafi da shi
- An gano gawarsa sa’o’i kaɗan bayan sace shi a ƙauyen Karau-Karau, inda aka ce an harbe shi a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zaria, Kaduna - Dr Iliyasu Abubakar Sadiq, malami kuma mai bincike a Sashen Noma na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ya rasa ransa bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi daga gidan gonarsa.
An yi garkuwa da malamin, wanda ya fito daga Jihar Jigawa, da misalin ƙarfe 10 na safe ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2027, daga gidan gonarsa da ke Tudun Muntsira, wata unguwa da ke bayan Samaru ta ABU.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano gawarsa da misalin ƙarfe 2 na rana a ƙauyen Karau-Karau.
Wasiyyar malamin ABU ta karshe
Kafin ’yan bindigar su tafi da shi, kalaman ƙarshe da Dr Sadiq ya yi wa matarsa, Hajiya Baraka, sun kasance roƙon ta da ta kula da ’ya’yansu.
“Baraka! Baraka! Ki kula da ’ya’yana. Don Allah, ki tausaya,” kamar yadda matar tasa ta ce ya riƙa maimaitawa yayin da ’yan bindigar ke jan sa daga gidan.
Malamin, wanda kuma manomi ne, yana da gonar itatuwa da gidan gona inda yake yawan zama tare da iyalinsa. Duk da cewa yana da gida a cikin rukunin gidajen jami’ar, wani lokaci yana kai iyalinsa gona kafin ya koma gidansa na aiki.
Yadda ’yan bindigar suka shiga
Da take ba da labarin abin da ya faru jiya, Baraka ta ce suna cikin gidan gonar ne kwatsam suka ji karensu yana ihu. Mijinta ya fito don ganin abin da ke faruwa, amma jim kaɗan ya dawo yana cewa, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
“Daga nan ya ce in taimaka masa mu rufe ƙofa. Yayin da muke ƙoƙarin rufe ƙofar, maharan suka turo daga waje domin su shiga. Suna cewa, ‘ku buɗe ƙofar ko mu shigo mu kashe ku,’” in ji ta.
A ƙarshe, maharan huɗu dauke da makamai suka fasa wani ɓangare na ƙofar, suka shiga gidan da ƙarfi.
Baraka ta ce mijinta ya yi ƙoƙarin guduwa, amma ’yan bindigar suka yi barazanar cutar da iyalinsa idan ya tsere.
“Sun gaya masa cewa ko da ya gudu, iyalinsa suna nan,” in ji ta.
Yadda mahara suka kashe Dr. Iliyasu
Ta ce maharan ba su rufe fuskokinsu ba, kuma dukkan huɗun suna ɗauke da bindigogi. Biyu daga cikin ’yan bindigar suka riƙe mijinta, yayin da sauran biyun suka juya gare ta, suna neman kuɗi.
“Na gaya musu cewa ba mu da kuɗi kuma ba mu ne masu wannan gona ba. Na ce mun zo ne kawai domin aiki. Da ba su yarda da ni ba, sai na ce su binciki gidan su ga ko akwai kuɗi,” in ji ta.

Source: Original
Daga nan ’yan bindigar suka nemi wayar mijinta da katin ATM. Baraka ta ce ta gaya musu cewa ba ta da damar shiga wayarsa ko bayanan asusunsa na banki.

Kara karanta wannan
Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira
“Da suka fahimci cewa ba mu da kuɗi, sai suka ce za su tafi da mijina. Mun roƙe su da su ƙyale shi, muna tunasar da su cewa muna da ƙananan yara da suke dogaro da shi, amma hakan bai hana su tafiya da shi ba.
“Bayan wasu sa’o’i, aka sanar da ni cewa an gano gawar mijina a kusa da ƙauyen Karau-Karau kuma an harbe shi," in ji ta.
An ceto ciyaman a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa an ceto Shugaban Karamar Hukumar Bungudu, Nura Umar Abdullahi, da wasu mutane 4 da suka tsere daga hannun ’yan ta’adda a Zamfara.
An ce mutanen sun tsere daga hannun masu garkuwa ne a yankin Karamar Hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, inda daga bisani sojoji suka shiga daji suka dauko su.
Asali: Legit.ng

