Ado Gwanja Ya Tabbatar da Ya Yi Rashin Lafiya, Ya Fadi Halin da Ya ke Ciki a Yanzu

Ado Gwanja Ya Tabbatar da Ya Yi Rashin Lafiya, Ya Fadi Halin da Ya ke Ciki a Yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Mawakin Hausa, Ado Gwanja, ya bayyana cewa ya warke daga rashin lafiyar da ta sa ya kwashe sama da wata biyu da barin asibiti
  • Gwanja ya ce bai da niyyar bayyana wa jama'a irin cutar da ya yi, yana mai cewa Allah ne Ya jarabce shi da ita kuma Shi ne Ya yaye masa ita
  • Mawakin ya kuma karyata wasu labaran da ake yaɗawa kan halin da yake ciki, yana mai cewa yanzu yana cikin ƙoshin lafiya kuma ya koma ci gaba da aikinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Mawakin Hausa kuma ɗan wasan Kannywood, Ado Gwanja, ya bayyana cewa ya warke daga rashin lafiyar da ta sa aka kwantar da shi a asibiti.

Gwanja ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce sama da wata biyu kenan da suka baro asibiti.

Kara karanta wannan

Matar Atiku ta shigo fage, Titi ta yi magana game da mulkin Shugaba Tinubu

Dan wasan Hausa, Ado Gwanja
Ado Gwanja a wani waje a Najeriya. Hoto: Ado Gwanja
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Gwanja ya ce ya yi rashin lafiya, amma hakan ba abin kunya ba ne, domin cuta daga Allah take kuma Shi ne Ya jarabce shi da ita.

Jinyar da Ado Gwanja ya yi

Mawakin ya ce abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda wasu ke ci gaba da yaɗa labaran cewa har yanzu yana cikin wani hali.

Ya ce babu wanda ya taɓa ganin hotonsa ko bidiyonsa a lokacin da yake jinya, saboda shi kansa bai bari a ɗauke shi hoto ko bidiyo ba.

Gwanja ya ƙara da cewa ko a lokacin da yake asibiti bai ɗauki hoto ko bidiyo da wayarsa ba.

Ya ce ba lallai ba ne ya bayyana wa jama'a irin cutar da ya yi, domin Allah ne Ya san sirrin jarabawar da Ya ɗaura masa.

Gwanja ya dawo bakin aiki

Gwanja ya bayyana cewa kwanaki uku da suka gabata ya fitar da sabuwar waƙar siyasa mai suna “Tabare”.

Kara karanta wannan

Ado Gwanja ya yi magana ana cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani

Ya ce manufar waƙar ita ce wayar da kan al'umma da jawo hankalin jama'a kan muhimman abubuwan da suka shafe su.

Mawakin ya ce wannan ne abin da yake yi yanzu, yana mai tabbatar da cewa ya ci gaba da aikinsa cikin ƙoshin lafiya.

Ya kuma yi kira ga gidajen jaridu da masu wallafa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su.

Mawakin Hausa, Ado Gwanja
Lokacin da Ado Gwanja ke wata waka. Hoto: Ado Gwanja
Source: Facebook

Ado Gwanja ya roƙi masoyansa da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa rashin lafiyar da ya fuskanta jarabawa ce daga Allah.

Ya kammala da gode wa masoyansa bisa addu'o'insu, ƙauna da goyon bayansu, yana mai cewa: “Alhamdulillah ina lafiya.”

An kashe Danshaganu a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil Danshagamu.

An kashe Danshagamu ne bayan wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kutsa gidansa da ke unguwar Gaida, a ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, inda suka kai masa hari da wasu abubuwa masu kaifi.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, bayan samun kiran gaggawa daga kwamandan ƙungiyar ’yan banga ta Gaida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng