Babban Yaron Dan Shagamu da Aka Kashe a Kano Ya Sha Alwashi kan Kisan Mahaifinsa

Babban Yaron Dan Shagamu da Aka Kashe a Kano Ya Sha Alwashi kan Kisan Mahaifinsa

  • Ammar Ibrahim Dan Shagamu ya ce shi da ’yan uwansa biyar na cikin tsananin baƙin ciki bayan kisan mahaifinsu
  • Ya ce wasu matasa da ake zargin yi wa mahaifinsa barazanar kisa suna hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike
  • Ammar ya yi gargaɗin kada a danganta kisan da siyasa ba tare da cikakken bincike ba, amma ya buƙaci a gurfanar da waɗanda suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Babban ɗan marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu, Ammar Ibrahim Dan Shagamu, ya buƙaci a yi wa mahaifinsa adalci.

Ammar Ibrahim Dan Shagamu ya bayyana cewa iyalinsa ba za su yafe wa waɗanda ke da hannu a mutuwarsa ba.

An kashe Dan Shagamu a Kano
Ibrahim Khalil Dan Shagamu da aka kashe a Kano Hoto: Ibrahim Khalil Dan shagamu
Source: Facebook

Babban yaron na Dan Shagamu ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna ta musamman da jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaban Amurka ya 'tsorata', ya fara laluben lokacin dakatar da yaki da ƙasar musulunci ta Iran

Ammar ya bayyana mutuwar mahaifinsa a matsayin babban rashi mai raɗaɗi, yana cewa shi da ’yan uwansa biyar har yanzu suna fama da jimamin abin da ya faru.

“Ni da ’yan uwana biyar yanzu mun zama marayu. Har yanzu muna cikin tsananin baƙin ciki da alhini saboda mutuwar mahaifinmu,” in ji shi.

An kira shi gida da labarin kisan mahaifinsa

Ammar ya ce ya bar gida kimanin shekaru huɗu da suka gabata, kafin a kira shi ba zato ba tsammani da labarin kisan mahaifinsa cikin mummunan yanayi.

“Bayan na bar gida shekaru huɗu da suka gabata, sai aka kira ni ba zato ba tsammani aka ce an kashe mahaifina cikin mummunan yanayi."

“Har yanzu ban fahimci cikakkun bayanan kisan ba, domin ban ma san cewa yana fuskantar barazana ba sai da na dawo gida bayan mutuwarsa,” in ji shi.

An ce ya fuskanci matsala da wasu mutane

A cewar Ammar, Dan Shagamu ya bar unguwae da suke zaune tun farko, inda kwanan nan ya koma Gaida ya zauna tare da wani abokinsa.

Kara karanta wannan

"A wasu lokutan," Ana zargin ba Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulkin Najeriya ba

Ya ce bayanan da ya samu daga wasu ’yan uwa sun nuna cewa mahaifinsa ya samu matsala da wasu mutane a unguwar.

A cewarsa, wasu daga cikin mutanen sun yi ƙoƙarin hana Dan Shagamu ba wa yaran unguwar sadaka da alewa, lamarin da ya haifar da rashin fahimta.

“Wannan rashin fahimtar ya sa wasu samari suka fara yi masa barazanar kisa,” in ji Ammar.

Ya ce mahaifinsa ya ɗauki bidiyon abin da ya faru sannan ya tura wa wasu ’yan uwa. A cewarsa, yanzu ana zargin waɗannan samarin da hannu a lamarin, kuma suna tsare a hannun ’yan sanda.

An ce mutane biyu sun shiga gidansa

Ammar ya ce iyalan har yanzu suna ƙoƙarin gano ainihin abin da ya faru a lokacin ƙarshe na rayuwar mahaifinsu.

Ya ce abin da maƙwabta da shaidun gani da ido suka iya gaya masa shi ne cewa an ga mahaifinsa yana shiga gidansa bayan sallar Magariba.

“Mutane biyu sun bi shi suka shiga cikin gidan. Bayan wani lokaci, mutanen biyu suka fito, amma shi bai fito ba. Wannan shi ne karo na ƙarshe da aka ga mahaifina da rai,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya kinkimo maganar kisan Sardauna, ya bayar da shawara

Sai dai ya ce babu wanda ya iya gaya wa iyalan ko su waye mutanen biyu, kuma shi ma bai san ko su ne mutanen da ake tsare da su a hannun ’yan sanda ba.

Ya yi gargaɗin kada a danganta kisan da siyasa

Ammar ya kuma yi kira da a guji yanke hukunci cewa kisan mahaifinsa na da alaƙa da siyasa ko wata ƙungiya kafin bincike ya tabbatar da hakan.

“Ko da yake ya kasance mai sukar gwamnati da ’yan siyasa, ba za mu iya cewa kisan nasa na da alaƙa da siyasa ko wata ƙungiya da wataƙila ya ɓata wa rai ba,” in ji Ammar.

Sai dai ya jaddada cewa abin da iyalinsa ke buƙata shi ne a gano waɗanda ke da hannu a kisan tare da tabbatar an yi musu adalci.

“Duk da haka, mun riga mun samu babban rashi, kuma babu abin da zai iya dawo mana da abin da muka rasa. Don haka, ba za mu yafe ba, domin rayuwar da aka ɗauka ba za a iya dawo da ita ba,” in ji shi.
Ana ta magana kan kisan Dan Shagamu a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamna Abba ya yi Allah wadai da kisan Dan Shagamu

Kara karanta wannan

'Yan uwan Dan Shagamu da aka kashe a Kano sun bayyana wani sirri kafin mutuwarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu.

Gwamna Abba ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gano tare da kama dukkan wadanda suke da hannu a aikata kisan domin a gurfanar da su a gaban doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng