Pantami: PDP Ta Shirya Fitar da Dan Takarar Gwamnan Jihar Gombe tsakanin Mutum 3
- Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa za a gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani na jihar Gombe ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026
- PDP ta tantance tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami, Khamisu Mailantarki da Usman Garry domin fafatawa a zaben da aka shirya
- Jam'iyyar PDP ta buƙaci mambobinta su guji jita-jita da kalaman da za su iya haifar da tashin hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Jam’iyyar PDP ta tantance Farfesa Isa Ali Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry domin su fafata a sabon zaɓen fitar da dan takarar gwamna na jihar Gombe.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar PDP a Gombe, Abdulkadir Ahmed Dukku, ya fitar ranar Juma’a.

Source: Facebook
Ya ce an tantance ’yan takarar ukun domin shiga sabon zaɓen fitar da gwani da za a gudanar biss umarnin babbar kotun tarayya, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta soke zaɓen fitar da dan takarar gwamnan da jam’iyyar ta gudanar a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, sannan ta umarci a sake gudanar da shi cikin wata guda.
PDP ta sanya ranar zaben fitar da gwani
Dukku ya ce:
“Bayan soke zaɓen, PDP na son sanar da dukkan mambobinta masu katin jam’iyya cewa za a gudanar da sabon zaɓen fitara da gwani na gwamnan ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026.
“Ana sa ran duk masu kaɗa ƙuri’a da suka cancanta za su taru a wuraren mazabunsu domin zaɓar ɗan takarar da suke so.”
A wata sanarwa ta daban, jam’iyyar ta ce ta karɓi hukuncin kotun cikin kyakkyawar fahimta tare da mutunta hukuncin, kamar yadd Leadership ta rahoto.
PDP ta yi maraba da hukuncin kotu
PDP ta kuma yi maraba da ɓangaren hukuncin da ya tabbatar da sahihancin kasancewar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami mamba, da kuma damar da ya samu ta shiga zaɓen fitar da gwani na watan Mayun 2026.
“Yanzu haka shugabancin PDP da ’yan takara suna nazarin hukuncin. Yayin da ake nazarin abubuwan da hukuncin ya ƙunsa ta fuskar doka da umarnin da ke cikinsa, muna kira ga dukkan mambobi, magoya baya da masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalinsu, su zauna lafiya kuma su kasance cikin haɗin kai,” in ji sanarwar.

Source: Facebook
PDP ta kare cancantar Pantami
Dukku ya ƙara da cewa hukuncin Kotun Ƙoli da Mai Shari’a Adamu Jauro ya karanta a yammacin ranar Alhamis bai shafi cancantar Farfesa Pantami na tsayawa takara a sabon zaɓen fitar da gwani ba.
Saboda haka, ya shawarci yan PDP da su guji jita-jita da kalaman da za su iya haifar da tashin hankali, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar za ta ɗauki duk matakan da suka dace bisa doka.
Pantami ya samu karin goyon baya
Kun ji cewa tsohon kwamishinan Gombe, Muhammad Ismail City ya fice daga APC tare da bayyana goyon bayansa ga Isa Ali Pantami a zaɓen gwamna na 2027.
Mohammed ya ce ƙwarewarsa a harkokin zaɓe da shugabancin ƙaramar hukuma ta ba shi damar fahimtar irin halayen da ake buƙata wajen samar da shugabanci nagari a jihar.
Asali: Legit.ng

