Yadda China ke Taimakon Iran Ta Ragargaji Amurka a Hormuz da Sauransu
- Wasu bayanan leƙen asiri da ƙungiyoyin China ke bai wa Iran sun taimaka mata wajen inganta iya gano wuraren sojojin Amurka da kai musu hare-hare
- Bayanan hotunan tauraron ɗan adam sun kuma taimaka wa Iran wajen bibiyar jiragen ruwa a mashigar tekun Hormuz da kuma barazana gare su da jirage marasa matuƙa
- Wasu jami’an Amurka sun ce taimakon China na daga cikin abubuwan da suka sa hare-haren Iran suka ƙara zama daidai a watannin baya-bayan nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Wasu rahotannin leƙen asirin Amurka sun nuna cewa bayanan hotunan tauraron ɗan adam da sauran bayanan leƙen asiri da ƙungiyoyin China sun taimaki Iran.
An ce kungiyoyin ne ke bai wa Iran taimako wajen inganta iya kai hare-haren soji kan wuraren Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Iska mai ƙarfi ta haddasa hatsarin jirgi, mata da dama sun rasa rayukansu a Najeriya

Source: Getty Images
Majiyoyi huɗu sun shaida wa CNN cewa taimakon ya kuma ƙara wa Iran damar yin barazana ga jiragen ruwa a mashigar tekun Hormuz da kuma kai hare-haren da suka fi daidaito kan sansanonin sojin Amurka.
'Yan China sun taimaka wa Iran
Majiyoyin sun ce bayanan hotunan tauraron ɗan adam sun taimaka wa Iran wajen kai hari kan wani sansanin Amurka da ke Jordan a watan Yuli, inda aka kashe sojojin Amurka uku.
A cewar jami’an Amurka, matakin da harin ya nuna na daidaito ya wuce abin da ake ganin Iran za ta iya cimmawa ba tare da irin wannan bayanan ba.
Wani jami’in Amurka ya ce bayanan ƙasa da sararin samaniya daga China sun kuma inganta damar Iran wajen bibiyar jiragen ruwa da ke ratsa mashigar Hormuz.
Iran na amfani da bayanan China
Majiyoyi biyu sun ce bayanan na taimaka wa Iran wajen amfani da wasu jirage marasa matuƙa masu bin zafin jiki, waɗanda ba za su iya sauya alkibla yayin da suke cikin iska ba.

Kara karanta wannan
"Za a iya cikin kwanaki 7"; Iran ta sanar da Amurka sharadin bude mashigar Hormuz

Source: AFP
Rahoton WSJ ya nuna cewa bayanan na taimaka wa sojojin Iran wajen sanin lokacin da ya fi dacewa su harba irin waɗannan jirage zuwa kan jiragen ruwa.
Jami’an Amurka sun ce fasahar jiragen ba ta da matuƙar rikitarwa, amma Iran ta ƙara nuna ƙwarewa wajen bibiyar ayyukan rakiyar jiragen ruwan Amurka da kuma kai hare-hare a lokacin da ya fi dacewa.
Jami’an Amurka sun ce Iran na kallon mashigar Hormuz a matsayin ɗaya daga cikin manyan wuraren da za ta iya amfani da su wajen matsa lamba.
Pakistan ta kai hari Afghanistan
A wani labarin, mun ruwaito cewa hare-haren sama da Pakistan ta kai kan Afghanistan sun kashe aƙalla mutum huɗu, yayin da gwamnatin Taliban ta yi barazanar mayar da martani.
Pakistan ta ce ta kai hare-hare kan wurare 10 a Afghanistan da ake amfani da su wajen ajiya da harba jirage marasa matuƙa, waɗanda wasu daga cikinsu ake zargin an yi amfani da su wajen kai hare-hare ta kan iyaka.
Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce hare-haren sun shafi lardunan Kandahar, Paktia da Khost, yayin da Ministan Yaɗa Labarai na Pakistan, Attaullah Tarar, ya tabbatar da su.
Asali: Legit.ng