Sabuwar Rigima: Sheikh Gumi da Mijin Matar Moroccoo Sun Shiga Kotu

Sabuwar Rigima: Sheikh Gumi da Mijin Matar Moroccoo Sun Shiga Kotu

  • Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya shigar da Nasiru Musa Idris kotu kan zarginsa da bata masa suna
  • Malamin ya shigar da ƙorafin ne a Babbar Kotun Shari'a ta Kaduna da ke Kawo bayan zarge-zargen da mijin matar ya yi a kafofin yada labarai
  • Sheikh Gumi ya jaddada cewa ya garzaya kotun shari'a ne domin neman hakkarsa tare da koya wa masu bata sunan jama'a darasi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – Shahararren malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Abubakar Gumi, ya garzaya kotu domin shigar da ƙorafin laifin ɓata suna a kan dan Najeriya da ya auri mata a kasar Morocco, Nasiru Musa Idris.

A cikin takardun kotu da aka fitar, Sheikh Gumi ya garzaya Babbar Kotun Shari'a ta Kaduna da ke zamanta a Kawo domin buƙatar fitar da sammacin laifi a kan wanda ake zargin wanda ke da addireshi a Suleiman Crescent, Kaduna.

Kara karanta wannan

An cafke Hafsat kan zargin yaɗa rahoton cewa Opay za su bar Najeriya

Matar Morocco da Sheikh Ahmad Gumi
Nasir Musa Idris da Sheikh Gumi a hagu da matar Morocco a dama. Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi|Nasir Musa Idris
Source: Facebook

Sheikh Ahmad Gumi ya wallafa takardun kotun a shafinsa na Facebook tare da fadin dalilin da ya sa ya ɗauki matakin neman haƙƙinsa ta hanyar shari'a.

Zargin da aka yi wa malamin

A cewar takardun ƙorafin, wanda ake zargi Nasiru Musa Idris ya gudanar da tattaunawa da gidajen jaridu da dama har da gidan talabijin da rediyo na RFI, inda ya watsa ƙarya a kan malamin.

Ya rubuta cewa:

"Ayyukan ɓata suna da zarge-zargen ƙarya suna lalata mutuncin mutum da matsayinsa a al'umma, kuma dole ne wadanda ke da hannu su fuskanci shari'a ta hanyar da ta dace. Wannan zai zama darasi ga kowa."

Abubuwan da korafin ya kunsa

Takardar kotun ta ƙara da cewa Nasiru Musa Idris ya zarge Sheikh Gumi da sace matarsa har na tsawon watanni 11, da ƙera hatimi na ƙarya, gami da satar dukiyoyinsa.

A cewar lauyoyin malamin, waɗannan zarge-zarge an yi su ne da nufin cutar da mutuncinsa da rage matsayinsa a idon duniya, wanda hakan ya saɓa wa sashi na 137 da 138 na tsarin dokar Shari'a ta jihar Kaduna ta shekarar 2002.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Daukar kirista a matsayin mataimakin gwamna ya tada ƙura a Arewa

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Sheikh Ahmad Gumi bayan wani taro da malamai a Kaduna. Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Lauyoyin malamin ƙarƙashin jagorancin M. T. Mohammed Esq. sun sanya hannu a kan takardar neman sammacin a ranar 8 ga Satumba, 2026.

Matar ba ta tare da Sheikh Gumi

A wani labarin daban, kun ji cewa lauyar matar dake cikin ce-e-ku-cen aure, Khadija Diab, ta fito ta ƙaryata zargincin da mijinta Nasiru Idris Musa ke yi na cewa tana tare da Sheikh Gumi.

Lauyar matar, Bilkisu Chedi, ta bayyana cewa Khadija ba ta tare da Sheikh Gumi ba saboda tun watan Afirilun shekarar 2026 take ƙasarta ta gida wato Maroko bayan ƙungiyarsu ta taimaka mata wajen samun takardar tafiya ta gaggawa.

Chedi ta ƙara da cewa kawar da matsalolin da mijin ya haifar ta hanyar ƙwace mata fasfo ne ya sa aka fitar mata da takardun, kuma a yanzu haka tana tare da iyalanta tsawon wata shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng