Kwastam Ta Yi Babban Kamu, an Ƙwace Mugayen Makamai da Aka Shigo da Su Ƙasa
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kwace bindigogi 204 da aka yi yunkurin shigowa da su ta Tin Can Island
- An boye bindigogin a cikin kwantena tare da kayan gida, yayin da binciken Kwastam ya gano bindigogin
- Kwastam ta ce amfani da bayanan sirri, fasaha, tantance hadari da haɗin gwiwa ya taimaka wajen dakile safarar makamai ba bisa ka’ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Hukumar Kwastam ta dakile shigowar makamai, ta kwace bindigogi 204 da aka yi fasa-kwaurinsu a Tin Can Port.
An kama wasu bindigogi 204 da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba da sassan makamai ga Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin ɗauka, NCCSALW.

Source: Twitter
Kokarin da hukumar Kwastam ke yi
Jami’an Rundunar Kwastam ta Tin Can Island ne suka gudanar da samamen, yayin da rundunar ta kara sa ido da amfani da bayanan sirri, cewar Punch.
Wannan ci gaba ya zo ne kimanin makonni biyu bayan Kwanturolan-Janar na Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya mika wa NCCSALW bindigogin JGF pump-action 399 da aka hada gaba daya da sassan bindigogi 535.
Adeniyi ya ce an tarwatsa bindigogin tare da boye su cikin sassan da aka rage girma, domin a wahalar gane su yayin duba kayan da ke cikin kwantena.
Ya ce daga baya binciken hukumar kwastam da hada sassan makaman ya tabbatar da cewa akwai bindigogi 399 da aka hada gaba daya da kuma wasu sassan bindigogi 535.
Daga cikin sassan makaman da aka gano akwai firam 89, hannayen caji 80, rukunin abin ja harsashi 579 da kuma makullan bindiga 25, cewar ThisDay.
Adeniyi ya ce kwace makaman na da matukar muhimmanci saboda kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, ciki har da ta’addanci, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da aikata laifuka masu tayar da hankali.
Ya kuma yi gargadin cewa shigowar makamai cikin kasar na iya zama babbar barazana ga tsaron jama’a da tsarin dimokuradiyya yayin da Najeriya ke kara kusantar wani lokacin gudanar da zabe.

Source: Original
Musabbabin samun nasarar hukumar Kwastam
Adeniyi ya ce dakile shigar makaman ya hana su isa inda aka nufa, tare da hana yiwuwar fadawa hannun miyagun laifuka, yayin da ake kokarin gano wadanda suka shigo da kayan da kuma wadanda za su karbe su.
Shugaban Kwastam ya danganta nasarar samamen da amfani da fasaha da tsarin tantance hadari karkashin shirin zamanantar da harkokin kasuwancin hukumar.
Ya jaddada cewa Kwastam ba za ta iya bude kowanne kwantena da ya shigo kasar domin gudanar da bincike na zahiri ba.
An karyata zargin Ribadu da safarar makamai
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NCCSALW ta karyata wani bidiyo da ke zargin Nuhu Ribadu, da daukar nauyin shigo da makamai.
Hukumar ta ce an kama mutane biyu dangane da makamai 399 da hukumar kwastam ta kama a tashar Tin Can Island.
Shugaban hukumar, DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a ciki da wajen Najeriya.
Asali: Legit.ng

