Peter Obi Ya Dawo da Zancen Zama Mataimakin Atiku Abubakar a ADC kafin Zabe
- Peter Obi ya bayyana cewa duk wata haɗaka ta siyasa yanzu ta sha gaban shi da Atiku Abubakar a daidaikunsu
- ‘Dan takarar ya kuma fayyace cewa shugabannin jam'iyya NDC da ADC ne kawai za su iya yanke shawarar haɗa-kai
- Obi ya jaddada cewa a shirye yake ya kasance a cikin haɗakar kawo ci gaba, aiki ga matasa da rage talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Peter Obi wanda yake rike da tutar Nigeria Democratic Congress (NDC) a 2027 ya yi zancen hadakar ADC.
Mista Peter Obi ya ce bai yi watsi da tayin zama mataimaki ga Atiku Abubakar a takarar shugaban kasa na 2027 ba.

Source: UGC
Hirar Peter Obi game da zaben 2027
‘Dan takaran shugaban kasar na NDC ya bayyana haka da aka zanta da shi a tashar Arise ranar Alhamis, 10 ga Satumba 2026.
Da farko an yi tunanin manyan ‘yan adawa za su hada kai a jam’iyyar ADC domin tunkarar Bola Tinubu da APC da kyau.
Peter Obi zai janye wa Atiku Abubakar?
The Cable ta ce ‘yan jarida sun tambayi Mista Obi shi ko zai iya zama abokin gamin Atiku ko kuma ya yafe masa takararsa.
Ba su dade a ADC bayan barin jam’iyyunsu ba, sai Peter Obi da magoya bayansa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NDC.
Tsohon gwamnan na Anambra ya ce yanzu zancen takara ya yi nisa kuma ya fi karfin a ce za su iya yanke mataki a daidaikunsu.
"Ni ‘dan takara ne, shi ma shugabana, Atiku ‘dan takara ne a wata jam’iyya.
"Ni ‘dan takaran wata jam’iyya ne. Saboda haka kana zancen jam’iyyu biyu su hada-kai ne; yanzu lamarin ya fi karfin ni ko shi."
- Peter Obi
Idan har za a hada-kai irin wannan, Obi ya ce sai jam’iyyun siyasar sun zauna a yi hadaka, ba iyaka masu neman takara ba.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi
Meyasa Obi bai zama mataimakin Atiku?
A matsayinsa na Peter, ya ce bai da ta-cewa idan ana maganar hakura da takara ko ya zama abokin tafiyar Atiku a zaben 2027.
Ya kuma yi karin haske cewa tun farko ba a zauna da shi har an yi masa tayin zama ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa ba.
‘Dan siyasar ya ce da an yi hakan ne da shi ne za a yi zancen ya karbi tayin ko akasin haka, labarin ya zo a jaridar Daily Post.
Hadakar da ke gaban Obi a zabe mai zuwa ita ce wanda za ta taimaka matasa su samu abin yi kuma ilmin zamani ya samu a kasar.

Source: Getty Images
'A zabi Atiku Abubakar a 2027' - Titi
Rahoto ya ce Titi Abubakar ta yi kiran a zaɓi Atiku Abubakar a 2027, ta fara haska wanda zai gaje shi idan ya gama mulki a Najeriya.
Ta caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ta ce al'amura sun lalace a kasar kuma talakawa suna fuskantar matsanancin halin rayuwa.
Titi ta kara da cewa ko da yake Atiku ya yi alkawarin shekaru hudu kacal zai yi, mutane za su roki ya cika wa'adinsa saboda gyaran da zai kawo.
Asali: Legit.ng
