Magu: Bukola Saraki Ya Samu Abin Magana da Kotu ta Wanke shi a Sabaninsa da Buhari

Magu: Bukola Saraki Ya Samu Abin Magana da Kotu ta Wanke shi a Sabaninsa da Buhari

  • Bukola Saraki, ya yi murnar hukuncin da ya soke tsawaita zaman Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC
  • Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ya ce matakin majalisar ba siyasa ba ne, illa dai sauke nauyin da aka ba su
  • Magu ya ci gaba da rike mukaminaa har zuwa Yuli 2020 duk da ‘yan majalisa ba su tabbatar da shi ba a lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin da ya haramta tsawaita wa’adin Ibrahim Magu da aka yi a hukumar EFCC.

Bukola Saraki ya ji dadin wannan, ya ce hakan ya gaskata matsayin da Majalisar Dattawa ta takwas ta ɗauka a karkashinsa.

Bukola Saraki
Bukola Saraki yana sallah tare da Muhammadu Buhari a Abuja da hoton Ibrahim Magu a ofis Hoto: Getty Images/EFCC
Source: UGC

Majalisa ta ki amincewa da Ibrahim Magu

Da yake magana a kafar Facebook bayan hukuncin a farkon makon nan, Dr. Bukola Saraki ya ce hukuncin kotun ya wanke shi

Kara karanta wannan

Majalisa za ta dauki mataki ganin Tinubu ya kara hutu ba tare da ba Kashim mulki ba

A lokacin yana shugaban majalisar dattawa ne fadar shugaban kasa ta tura Ibrahim Magu domin a tantance shi a kujerar EFCC.

Sau biyu Majalisar dattawa tana korar Ibrahim Magu, ta ki amincewa da nadin shi a matsayin cikakken shugaba na EFCC.

Gwamnati ta bar Magu a ofis har 2020

Ganin matakin da majalisar Bukola Saraki ta dauka a 2016 da 2017, an zarge shi da kawo tasgaro wajen yaki da rashin gaskiya.

Duk da ba a sahale masa cigaba da rike mukamin ba, Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bar Magu a hukumar EFCC ta kasa.

Saraki ya koka cewa Magu ya cigaba da rike matsayin nan har zuwa Yulin 2020 ba tare da izini ba.

Ya ce:

“Jiya, kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa tsawaita wa Magu wa’adin zama shugaban EFCC na riƙo ya saba wa doka.
Bayan kusan shekaru 10, na sake jin cewa an tabbatar da cewa abin da na tsaya a kai tun farko gaskiya ne,”

Kara karanta wannan

Abubuwan da Shettima ya fada kan Najeriya a taron majalisar dinkin duniya

Saraki ya fadi kalubalen da suka fuskanta

‘Dan majalisar ya ce ba siyasa suka duba wajen daukar wannan mataki ba, suna yin aikin da dokar kasa ya ba su hurumin yi ne.

Ganin sukar da ya sha daga jama’a da suke ganin sabanin siyasa ta yi tasiri, Saraki ya yi farin ciki a yanzu kotu ta wanke su.

“A wancan lokacin, wasu sun kira matakin da muka dauka da na siyasa. Amma ba haka ba ne. Abin da muka yi shi ne kawai amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba mu, tare da tsayawa kan abin da muka yi imanin shi ne daidai.
“Ni da abokan aikina a Majalisar Dattawa ta takwas, da iyalanmu da kuma mutanen da ke tare da mu, mun fuskanci abin da ba zan iya kwatantawa da wani abu ba face kokarin da Magu ya yi na razana mu,”

- in ji shi.

Jawabin yana nan a shafinsa na X bayan alkalan kotun daukaka kara sun yi hukunci a Abuja.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

A karshe ya ce darasin da ya dauka shi ne a duk abin da zai faru idan mutum yana kan mukami, ya tsaya a kan ka’dojin aiki.

bukolasaraki
Bukola Saraki. Yakubu Dogara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Majalisar Tarayya hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Majalisa na son a ba Shettima mulki

Rahoton nan kuwa ya ce wasu ‘yan majalisa suna so da karfi da yaji a mika wa Kashim Shettima shugabanci na rikon kwarya

A doka, an ce bai kamata Bola Tinubu ya shafe kwanaki sama da 21 bai kasar da sunan hutu ba, har yanzu kuwa yana turai.

Ana so Sen. Godswill Akpabio da Rt. Hon. Abbas Tajudeen su bude majalisa domin a ba Kashim Shettima mulkin rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng