Sarkin Musulmi Ya Bukaci Kowa Ya Fita Duba Watan Rabi'ul Sani 1448 a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Bukaci Kowa Ya Fita Duba Watan Rabi'ul Sani 1448 a Najeriya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmin Najeriya su fara neman jinjirin watan Rabi’ul Sani 1448H a ranar Juma’a, 11 ga Satumba 2026
  • Sarkin Musulmin ya bukaci Musulmi su fara duban jinjirin wata nan da nan bayan faduwar rana, tare da kai rahoton ganin watan ga hukumomin da suka dace a yau
  • A sanarwar da ya fitar, Sarkin ya bayyana cewa za a tantance duk wani rahoton ganin wata kafin a fitar da sanarwar hukuma kan shiga watan Rabi’ul Sani na 1448H

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmin ƙasar nan da su nemi jinjirin watan Rabi’ul Thani 1448H a ranar Juma’a, 11 ga Satumba 2026.

Kara karanta wannan

An cafke dan sandan bogi da ya shiga Kano ya rika damfarar jama'a

Sanarwar umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Wazirin Sokoto kuma Shugaban Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini na Masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanya wa hannu.

Mai alfarma sarkin Musulmi
Sarkin Musulm a hagu da wata a dama. Hoto: Getty Images|JNI
Source: Facebook

Sanarwar da fadar ta walllafa a Facebook ta ce ranar Juma’a, 11 ga Satumba ta yi daidai da 29 ga Rabi’ul Awwal 1448H, don haka ita ce ranar da ta dace Musulmi su nemi sabon jinjirin wata.

Yadda za a kai rahoton ganin wata

Vanguard ta wallafa cewa Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmi a faɗin ƙasar su sa ido kan jinjirin wata da zarar rana ta fadi.

Ya umurci duk wanda ya ga jinjirin watan da ya gaggauta kai rahoton zuwa ga Dagaci ko Hakimin yankinsa domin a isar da shi ga Sarkin Musulmi.

Sanarwar ta jaddada muhimmancin gabatar da ingantaccen rahoto, inda ta ce za a bincika tare da tantance sahihancin duk wani rahoton ganin wata kafin a tabbatar da shi.

Gargadi kan rahoton ƙarya

Masarautar Sokoto ta kuma yi gargadi kan yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da su ba ko kuma yin sanarwar fara watan tun kafin lokacin.

Kara karanta wannan

Rigimar El Rufai da ministan tsaro: Jama'atu Nasril Islam da CAN sun tsoma baki

Ta bukaci Musulmi su gudanar da aikin neman jinjirin watan cikin gaskiya, muhimmanci da kuma fahimtar nauyin da ke kansu na addini.

Bayan tabbatar da ganin jinjirin watan, Sarkin Musulmi ne zai fitar da sanarwar hukuma da za ta tabbatar da fara watan Rabi’ul Sani 1448H.

Umarnin na Sultan ana sa ran zai sa Musulmi, sarakunan gargajiya da shugabannin addini a faɗin ƙasar su shiga aikin neman jinjirin watan.

Ta'aziiyar Sarkin Gumel

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gumel na jihar Jigawa, Alhaji (Dr.) Ahmed Muhammad Sani II, CON.

Marigayin ya rasu ne ranar Alhamis, 3 ga Satumba 2026, a birnin Alkahira na ƙasar Masar, bayan ya shafe shekaru 46 yana kan karagar mulkin Gumel.

Sarkin Musulmi ya bayyana marigayin a matsayin babban malami, mai hikima kuma uba ga al'umma, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga Masarautar Gumel, jihar Jigawa da al'ummar Musulmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng