Wakilan Kasashen Duniya Sun Kunyata Netanyahu a Taron UNGA

Wakilan Kasashen Duniya Sun Kunyata Netanyahu a Taron UNGA

  • Wakilan ƙasashe da dama sun fice daga zauren Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fara jawabi
  • Wasu daga cikin wakilan sun yi ihu da fito, yayin da wasu suka tsaya suna tafi ga Netanyahu yayin jawabin
  • Netanyahu ya kare harin Isra’ila kan Iran tare da sukar Turkiyya, wasu ƙasashen Turai da kuma magajin garin New York, Zohran Mamdani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin New York, Amurka - Wakilai daga ƙasashe da dama sun fice daga zauren Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fara gabatar da jawabinsa ranar Alhamis.

Ficewar wakilan ta maimaita irin zanga-zangar da aka gudanar a lokacin da Netanyahu ya gabatar da jawabinsa a zaman Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na bara.

Netanyahu ya sha ihu a taron UNGA
Netanyahu na jawabi a taron UNGA karo na 81 Hoto: Alexi J. Rosenfeld
Source: Getty Images

Yayin da dimbin jami’an diflomasiyya suka fice daga zauren, wasu kuma sun tsaya suna tafa wa shugaban gwamnatin Isra’ila.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sauya dabara, ta cafke kasurgumin jagoran 'yan ta'adda

An yi wa Netanyahu ihu a zauren

Wasu daga cikin wakilan sun yi ihu da fito yayin da Netanyahu ke fara jawabi, yayin da ’yan tawagarsa suka tsaya suna tafa masa.

Mai jagorantar zaman ya kuma yi ta neman a kwantar da hankali tare da kiran jama’a da su kiyaye doka da oda a zauren.

Wasu daga cikin magoya bayan Netanyahu sun rika rera taken “Am Yisrael Chai”, wato “Al’ummar Isra’ila na nan da rai”.

Netanyahu ya mayar da martani ga wakilan da suka fice, inda ya kira su da “masu tsoro marasa ɗabi’a”.

“Idan akwai wasu masu tsoro marasa ɗabi’a da ba su bar wannan zauren ba tukuna, don Allah ku fita yanzu,” in ji Netanyahu.

Netanyahu ya kare yaƙin Iran

Firaministan na Isra’ila ya kuma kare matakin ƙasarsa na kai hari kan Iran. Ya ce da a ce Isra’ila ba ta kai harin ba, “da dukkanmu mun mutu”.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

Netanyahu ya ce lalata cibiyoyin nukiliyar Iran abu ne mai matuƙar wahala, amma a matsayinsa na firaminista, ya ɗauki matakin a matsayin ɗaya daga cikin shawarwari mafi sauƙi da ya taɓa yanke wa.

Ya kuma ce faduwar gwamnatin Iran “abu ne da lokaci kaɗai ya rage”, yana mai cewa al’ummar Iran za su samu ’yanci wata rana.

Ya soki ƙasashen Turai da Turkiyya

Netanyahu ya kuma soki wasu ƙasashen Turai kan matakin sanya takunkumi kan matsugunan Isra’ila da ke Yammacin Kogin Jordan da ake mamaye da shi.

Ya kuma kai wa Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, hari da kalamai, inda ya kira shi “azzalumi” tare da zarginsa da karɓar shugabannin Hamas.

“Ƙasa ta baya-bayan nan da ta zama babbar mai yaɗa ƙaryace-ƙaryacen kyamar Yahudawa ita ce Turkiyya... Erdoğan azzalumi ne. Yana kuma karɓar shugabannin Hamas,” in ji shi.

Netanyahu ya ambaci Yahudawa da ke New York

Firaministan Isra’ilar ya kuma yi iƙirarin cewa “Yahudawa da dama” ba sa jin cewa suna cikin aminci a New York tun bayan zaɓen Zohran Mamdani a matsayin magajin garin.

“Tun lokacin da aka zaɓe ka a matsayin magajin wannan birni, Yahudawa da dama ba sa jin cewa suna cikin aminci a New York,” in ji Netanyahu.

Kara karanta wannan

"Ta wata hanya daban"; Kwankwaso ya ce za su dawo da tallafin man fetur

Ya kuma zargi Mamdani da yin abin da ya kira zargin ƙarya da maimaitawa kan Isra’ila da cewa tana aikata kisan kiyashi.

An yo ihu ga Netanyahu a UNGA
Wakilai kasashen duniya na ficewa daga taron UNGA don adawa da Netanyahu Hoto: Bryan Murphy
Source: Getty Images

Amurka za ta sayar da makamai ga Israila

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta shirya sayar da makamai masu yawa ga babbar kawarta Israila.

Gwamnatin ta Trump n kan hanyar amincewa da wani kunshin makamai da darajarsa ta kai dala biliyan 2.8 da za a sayar wa Isra’ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng