Abin da Mu Ka Sani kan Batun Mutuwar Tsohon Gwamnan Bauchi, Isa Yuguda

Abin da Mu Ka Sani kan Batun Mutuwar Tsohon Gwamnan Bauchi, Isa Yuguda

  • Wani makusancin tsohon Gwamnan Bauchi Isa Yuguda ya yi magana kan rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan ya rasu
  • Salisu Barau ya bayyana halin da tsohon gwamnan na jihar Bauchi yake ciki yayin da yake mayar da martani kan jita-jitar mutuwarsa
  • Isa Yuguda ya kasance Gwamnan Bauchi daga 2007 zuwa 2011, sannan ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Sufurin Jiragen Sama na Tarayyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - An yada wata jita-jita da ke ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya rasu ya bar duniya.

Wani makusancinsa ya fito ya karyata wani rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan na jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda, ya rasu.

Isa Yuguda na nan da ransa
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda Hoto: Isa Yuguda
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce wani makusancinsa, Alhaji Salisu Barau, ya bayyana rahoton a matsayin tsabagen ƙarya da babu tushe a cikinsa.

Kara karanta wannan

"Allah ne ya cece ni," Gwamna ya ba da labarin yadda aka yi yunkurin kashe shi a gidansa

Alhaji Salisu Barau ya bayana cewa Isa Yuguda wanda ya yi mulki a wa'adi biyu yana raye kuma yana cikin ƙoshin lafiya.

Makusanci ya ce Yuguda yana raye

Da yake magana da jaridar ta waya ranar Juma’a, 25 ga watan Satumban 2026, Salisu Barau ya ce babu kamshin gaskiya a cikin rahoton da ke cewa tsohon gwamnan ya rasu.

Alhaji Salisu Barau ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta.

“Ƙarya ce; Mallam Isa Yuguda yana cikin ƙoshin lafiya,” in ji Alhaji Salisu Barau.

Haka kuma, wani makusancin tsohon gwamnan kuma tsohon mai taimaka masa, Hon. Abdulmumini Kundak, ya karyata rahoton.

Hon. Abdulmunini Kundak ya bayyana labarin a matsayin bayanan ƙarya da babu kamshin gaskiya ko kadan a cikinsu.

Tarihin Isa Yuguda

An haifi Isa Yuguda ranar 15 ga Yuni, 1956. Ya zama Gwamnan Jihar Bauchi daga shekarar 2007 zuwa 2015, inda ya jagoranci jihar na tsawon wa’adin shekaru huɗu har sau biyu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya jawo wa kansa rigima da ya taba gwamnan Benue

Kafin zama gwamna, Yuguda ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Sufurin Jiragen Sama na Tarayya daga watan Mayun 2003 zuwa Yunin 2005.

Matsayinsa a siyasa

Tsohon gwamnan ya kuma taɓa kasancewa Jakadan Renewed Hope kuma Mai Kula da ayyukan wannan tafiya a yankin Arewa maso Gabas.

A halin yanzu, Yuguda mamba ne na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a tarayyar Najeriya.

Rahoton mutuwarsa ya fara yawo ne a kafafen sada zumunta, amma mutanen da ke kusa da tsohon gwamnan sun musanta labarin, suna mai cewa yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya.

Isa Yuguda bai mutu ba
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tsohon gwamnan Kogi ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu ya koma ga Mahaliccinsa.

Marigayi Alhaji Ibrahim Idris ya rasu ne ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2026, a kasar Birtaniya yana da shekaru 77.

Ibrahim Idris ya zama gwamnan jihar Kogi a watan Mayun 2003, bayan ya lashe zaben gwamna karkashin jam’iyyar PDP. Ya sake lashe zaben shekarar 2007, inda ya ci gaba da mulkin jihar a wa’adinsa na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng