Ba Boye Boye Kungiyar Malaman Addini Ta Bayyana Dalilin Goyon Bayan Tinubu a 2027
- Charismatic Bishops Conference of Nigeria ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu domin neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027
- Shugaban ƙungiyar, Leonard Kawas, ya yaba wa Tinubu kan naɗa Kiristoci a muhimman mukamai a gwamnatin tarayya
- Kawas ya ce Tinubu ya samu nasarar daidaita bambancin addini da sauran bambance-bambancen Najeriya, yana mai cewa babu nuna son kai a gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ƙungiyar Charismatic Bishops Conference of Nigeria (CBCN) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya nemi wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Bishof-bishof ɗin sun bayyana matsayar ne yayin taron majalisar ƙungiyar na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Source: Getty Images
Akume da Idris sun halarci taron
Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
Wakilan CBCN daga shiyyoyi shida na Najeriya ne suka buƙaci shugaban ƙungiyar, Leonard Kawas, ya bayyana matsayar da taron ya cimma kan zaɓen 2027.
Kawas ya bayyana dalilin goyon bayan Tinubu
Kawas ya ce CBCN na da mambobi a ƙasashe 52, yayin da Najeriya kaɗai ke da bishof 950 da ƙungiyar ta bayyana a matsayin “canonical”.
Ya ce CBCN na daga cikin ƙungiyoyin da suka nuna damuwa kan tikitin takarar shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi da APC ta yi amfani da shi a zaɓen 2023.
Sai dai Kawas ya ce Tinubu ya ba su mamaki ta hanyar naɗa Kiristoci a wasu muhimman mukamai a gwamnatinsa.
A cewarsa, hakan ya sa Kiristoci suka fara sauke fargabar da suka yi game da tsarin gwamnatin Tinubu.
An yaba wa naɗin Akume da Wike
Kawas ya ce naɗin George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya na daga cikin abubuwan da suka sauya ra’ayinsu.
“Nan take, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara fitar da sunayen waɗanda zai naɗa. Kafin mu ankara, aka naɗa wani Kirista da dukkanmu muke ƙauna, Sanata George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya,” in ji shi.
Ya kuma yaba da naɗin Nyesom Wike, Kirista, a matsayin Ministan Abuja, yana mai cewa hakan ya ƙara rage damuwar da suka samu tun bayan zaɓen 2023.
Kawas ya ce bayan sun duba yadda Tinubu ya tafiyar da al’amuran ƙasa, sun fahimci cewa shugaban ya yi ƙoƙarin daidaita bambancin addini da sauran bambance-bambancen da ke akwai.
An yaba da naɗin Nentawe Yilwatda
Kawas ya kuma ce Tinubu ya taimaka wajen naɗa Nentawe Yilwatda, wanda Kirista ne, a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Ya ce shugaban ƙasar ya kuma goyi bayan ’yan takarar Kirista da suka samu damar zama gwamnonin jihohi.
Bishof-bishof sun yi wa Tinubu alƙawarin goyon baya
Kawas ya ce ƙungiyar ta hallara domin sake tabbatar wa Tinubu da cikakken goyon bayanta, tare da ci gaba da yi masa addu’a da kuma tallata shirye-shiryen da yake ganin za su taimaka wajen ci gaban Najeriya.
Daga ƙarshe, Kawas ya bayyana cewa taron CBCN ya amince da Tinubu a matsayin wanda ƙungiyar za ta goya wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Tinubu ya ba malamai shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da muhimmiyar shawara ga malaman addinin Kirista a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bukaci shugabannin Kirista su inganta zaman lafiya da shiga zaɓe cikin mutunci ba tare da cin zarafi ba.
Asali: Legit.ng

