Bauchi: Rikici Ya Barke a APC, 'Yan Takara Sun Yi Zargin an Sauya Sunayensu
- Wasu ’yan takarar APC a Bauchi sun zargi jam’iyyar da sauya sunayensu bayan sun yi nasara a zaɓen fidda gwani na 2026
- Rikicin ya ƙara tsananta ne yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyar ke ci gaba da yin murabus, suna zargin rashin adalci da tilasta ’yan takara
- Shugabancin APC na Bauchi ya ce zai binciki zargin sauya sunayen ’yan takara, yayin da jam’iyyar ta ce tana da ƙarfin magance matsalolinta na cikin gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Sabon rikici ya ɓarke a cikin jam’iyyar APC Jihar Bauchi bayan wasu ’yan takarar Majalisar Dokokin Jihar sun zargi jam’iyyar da sauya sunayensu bayan sun yi nasara a zaɓen fidda gwani.
Rikicin ya ƙara bayyana samun ɓangarori a cikin jam’iyyar, musamman yayin da wasu jiga-jiganta da masu neman takara ke yin murabus tare da ƙorafe-ƙorafen rashin bin tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa rikicin ya sanya wasu daga cikin kusoshin jam'iyyar APC a Bauchi sun fice daga cikinta.
Dan takara ya zargi APC da sauya sunansa
Ɗaya daga cikin ’yan takarar da abin ya shafa shi ne Hon. Abdulhamid Rufai, wanda ke neman komawa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi domin wakiltar mazabar Zungur/Galambi/Miri.
Rufai, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar, ya ce an gudanar da zaɓen fidda gwani ranar 21 ga Mayu 2026, sannan aka bayyana sakamakon ranar 23 ga Mayu.
Ya ce an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani, sannan shi da sauran ’yan takara suka cika takardun da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buƙata.
Sai dai ya ce ya yi mamaki lokacin da INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takara, inda bai ga sunansa ba.
Rufai ya yi zargin cewa sauya sunansa na iya kasancewa da alaƙa da ƙoƙarin wasu jiga-jigan jam’iyyar na shigar da mutanen da suke goyon bayansu.
’Yan takara uku sun ce an sauya sunayensu
Rufai ya kuma yi zargin cewa wasu ’yan takara biyu daga ƙaramar hukumar Ganjuwa sun fuskanci irin wannan matsala.
Su ne Zulkifilu Dahiru Kafi, wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe mazabar Ganjuwa ta Yamma, da Ibrahim A. Adamu, wanda ya yi nasara a Ganjuwa ta Gabas.
A cewar Rufai, dukkan ’yan takarar uku sun cika takardun INEC kafin daga bisani a sauya sunayensu.
Ibrahim A. Adamu shi ma ya yi zargin cewa an soke nasararsa a mazabar Ganjuwa ta Gabas ta hanyar sauya sunansa.
Rikicin tikitin gwamna ya ƙara dagula APC
Rikicin bai tsaya kan ’yan takarar majalisar dokoki kaɗai ba, domin magoya bayan tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, sun nemi shugabancin APC na ƙasa ya sake duba yadda tsohon Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ya samu tikitin takarar gwamna na 2027.
Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓen Tuggar ta zargi rashin bin ƙa’ida a tsarin da ya haifar da nasarar Abubakar, inda ta nemi Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya maye gurbinsa da Tuggar.
Jiga-jigan APC na ci gaba da yin murabus
A yayin da ake fama da wannan rikici, wasu fitattun ’yan jam’iyyar sun fice daga APC. Daga cikinsu akwai tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Alhaji Sagir Aminu Saleh; tsohon ɗan takarar gwamna na APC sau biyu, Captain Muhammad Bala Jibrin; da Hon. Sunusi Aliyu Kunde, wanda ke da kusanci da Ambasada Tuggar.
Bala Jibrin ya danganta murabus ɗinsa da rikicin cikin gida na jam’iyyar, yana zargin “rashin adalci a fili” da kuma tilasta ’yan takara ba tare da la’akari da ’yan jam’iyya da mazaɓunsu ba.
Tun bayan zaɓen fidda gwani, wasu ’yan APC da dama sun kuma fice daga jam’iyyar, ciki har da Hon. Rabilu Bala Kashuri da Hon. Tijjani Mohammed Aliyu.
Asali: Legit.ng


