Rigima Ta Kara Zafi: Gwamna Dauda Ya Tura Zazzafan Sako ga Wike
- Dauda Lawal ya bukaci Nyesom Wike ya bayyana matsayarsa ta siyasa kan alaƙarsa da Rainbow Coalition da kuma goyon bayan Shugaba Bola Tinubu
- Gwamnan ya ce gwamnonin APC sun tsaya kan matsayarsu na goyon bayan jam’iyyar, yana mai cewa Wike dole ne ya bayyana inda yake a siyasance
- Wike ya sake tabbatar da goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu, duk da cewa yana da alaƙa da ’yan takarar PDP a wasu jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin New York, Amurka -Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya fayyace matsayarsa ta siyasa dangane da alaƙarsa da Rainbow Coalition.
Lawal ya ce Wike ba zai iya kasancewa yana goyon bayan jam’iyyar APC a lokaci guda yana tallafa wa wasu jam’iyyun siyasa ba.

Source: Facebook
Dauda Lawal ya ce Wike ya zaɓi ɓangare ɗaya
Gwamna Dauda ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da shirin Inside Sources na Channels Tv a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 da aka gudanar a New York.
Wike, wanda ɗan jam’iyyar PDP ne, yana da alaƙa da Rainbow Coalition, wata ƙungiyar siyasa da ta haɗa ’yan jam’iyyu daban-daban domin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Gwamna Dauda Lawal ya ce ya kamata Wike ya fayyace inda akalarsa ta siyasa take.
“Saƙonmu a bayyane yake sosai, ka kasance a gefe ɗaya. Ba za ka iya kasancewa a ɓangarori biyu ba. Idan kana APC, ka fito fili ka goyi bayan APC, ba wai kana goyon bayan APC a nan sannan kana goyon bayan wasu jam’iyyu a wani wuri ba,” in ji shi.
Gwamnan ya ce gwamnonin APC ba za su sauya matsayarsu ba, ko da kuwa Wike ya ci gaba da bayyana nasa ra’ayin kan batun.
“Muna nan kan matsayarmu kuma saƙon a bayyane yake. Zai iya magana, ya faɗi duk abin da yake so, amma matsayarmu a bayyane take, APC gaba ɗaya daga sama har ƙasa,” in ji shi.

Kara karanta wannan
A kai kasuwa: Jigo a APC ya watsawa gwamna kasa a ido, ya ki karbar mukamin da ya ba shi
Lawal ya ce Wike ya koma APC
Da aka tambayi Gwamnan Zamfara ko matsayar gwamnonin APC na nufin suna neman Wike ya koma jam’iyyar APC, Dauda Lawal ya amsa da cewa, “hakkun.”
Ya kuma ce zai tattauna batun matsayar Wike da Shugaba Tinubu bayan shugaban ya dawo daga hutun aiki da yake yi a Faransa.
“Wannan wani abu ne da zan tattauna da shugaban ƙasa idan ya dawo. A samu tsayayyar magana kan inda wannan mutumin yake. Ko yana APC ko ba ya cikinta, abu ne mai sauƙi. Don haka zan tafi tare da ’yan uwana gwamnonin.” In ji shi.

Source: Facebook
Wike ya raba gwamnonin APC 2
A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin siyasa tsakanin Nyesom Wike, da wasu daga cikin gwamnonin APC ya raba gwamnonin jam’iyyar zuwa sansanonin siyasa daban-daban gabanin zaben 2027.
Yayin da wasu gwamnonin ke nuna goyon baya ga Wike, wasu kuma sun jingina da Hope Uzodimma da AbdulRahman AbdulRazaq a rikicin da ke kara tsananta.
Asali: Legit.ng
