Babbar Magana: Amurka Ta Shigo da Manyan Makamai da Kayan Aiki cikin Najeriya
- Amurka ta bai wa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya kayan aikin soja domin taimakawa ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci a Arewacin Najeriya
- An kawo kayan wadanda suka kunshi maiamai a ranar Lahadi, 6 ga watan Satumba, 2026 ta cikin jirgin sojin saman Amurka C-17
- Isowar kayan ya zo ne wata guda bayan tawagar Najeriya karkashin jagorancin NSA Nuhu Ribadu ta halarci taron hadin gwiwa a Washington DC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙasar Amurka ta kawo kayan aiki da suka kunshi makamai da sauransu ga Rundunar Sojin Sama ta Najeriya.
Amurka ta shigo da kayan aikin soja Najeriya ne wata guda bayan mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa birnin Washington DC.

Source: Twitter
Jaridar Nigeria Stories ta wallafa hotunan kayan aikin da Amurka ta shigo da su Najeriya domin tallafa wa rundunar sojojin sama wajen yaki da kungiyoyin yan ta'adda a shafinta na X.
Dalilin kawo kayan aiki ga Najeriya
Hakan ne na zuwa ne bayan tawagar Najeriya da Amurka sun yi wata ganawa ta kwamitin hadin gwiwar kasashen biyu kan tsaro a Washington DC.
An kawo kayan aikin ne ranar Lahadi, 6 ga watan Satumba, ta cikin wani jirgin sojin saman Amurka kirar C-17.
Kayan aikin na cikin yarjejeniyar sayar da kayan aikin soja tsakanin ƙasashen biyu, wadda ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Amurka da Najeriya.
Haka kuma, kayan za su taimaka wa Najeriya wajen ƙoƙarin da take yi na yaƙi da ta’addanci a arewacin ƙasar.
Amurka ta sanar da kawo kaya Najeriya
Rundunar Sojin Amurka mai kula da Afirka (AFRICOM) ta bayyana a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis cewa an kawo kayan aikin ne a watan Satumba ta hanyar jirgin saman sojin saman Amurka C-17.
Rundunar ta ce:
“Kawo kayan aikin zai kara karfafa hadin gwiwar dabarun tsakanin kasashen biyu domin inganta kokarin da Najeriya ke jagoranta na yaki da ta’addanci a yankin.
"Tallafin sojin Amurka ga Rundunar Sojin Najeriya ya samo asali ne daga gayyatar Najeriya, kuma ya ginu ne kan mutunta ikon mallakar Najeriya.”

Source: Twitter
Amurka ta janye sojojinta dag Najeriya
A watan da ya gabata, Dagvin Anderson, kwamandan AFRICOM, ya sanar da cewa Amurka ta janye da dama daga cikin sojojinta da ke Najeriya, kamar yadd The Cable ta rahoto.
Hakan ya biyo bayan samamen da aka gudanar a watan Mayu wanda ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, mataimakin kwamandan kungiyar ISIS, a yankin tafkin Chadi.
Jami’an Amurka da Najeriya sun ce duk da cewa adadin sojojin da aka tura zuwa kasar ta Yammacin Afirka ba shi da yawa, sun samu gagarumar nasara.
Dalilin kin cire Najeriya daga CPC
Kun ji cewa dan majalisar dokokin Amurka ya jaddada cewa bai kamata kasar ta cire Najeriya daga ƙasashen da ake zargi da take ’yancin addini ba.
Riley Moore ya ce karuwar kashe Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna akwai buƙatar ci gaba da matsa wa Najeriya lamba.
Asali: Legit.ng

