Shugaban Amurka Ya 'Tsorata', Ya Fara Laluben Lokacin Dakatar da Yaki da Kasar Musulunci Ta Iran
- Shugaba Donald Trump ya yi hasashen cewa yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Iran zai ƙare nan take bayan zaɓen tsakiyar wa’adi na Nuwamba
- Trump ya ce kasar Iran ba za ta iya jure matsin tattalin arzikin da Amurka ke yi mata na dogon lokaci ba
- Rikicin ya ƙara yin barazana ga jigilar kayayyaki da samar da makamashi yayin da hare-hare suka tsananta a yankin mashigar Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi hasashen cewa yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da kasar musulunci ta Iran zai ƙare bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka na watan Nuwamba, 2026.
Shugaba Trump ya bayyana haka ne yayin da kassshen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa da ƙarin hare-hare kan jiragen ruwa a yankin, musamman a mashigar ruwa ta Hormuz.

Source: Getty Images
Tribune Nigeria ta ce Trump ya yi wannan hasashen ne ranar Laraba yayin da rikicin ya shiga wata na bakwai, yana mai cewa Iran ba za ta iya jure ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki daga Amurka ba.
Yaushe yakin Amurka da Iran zai kare?
“Ina ganin yaƙin zai ƙare nan take bayan zaɓen wa'adi,” in ji Trump, yana mai cewa Tehran na ƙoƙarin yin tasiri kan zaɓen Nuwamba, amma daga ƙarshe ba za ta iya ci gaba da yaƙin ba.
Kalaman shugaban Amurkan sun zo ne a lokacin da rikicin ya shiga wani yanayi mai tsanani, inda hare-hare suka shafi jiragen dakon mai da na kasuwanci a kusa da mashigar Hormuz.
Iran ta ce ta kai hari kan jiragen ruwa 10 da ke kusa da mashigar ruwa mai muhimmanci, bayan da Amurka ta lalata jiragen dakon man fetur biyar na Iran.
Yadda farashin danyen mai ya tashi

Kara karanta wannan
Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya
Rikicin ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi, inda farashin gangar ɗanyen man Brent ya haura dala 100 a baya-bayan nan, a karon farko tun watan Yuli.
Trump ya ce yana sa ran farashin mai zai ragu bayan kawo ƙarshen rikicin, amma ya amince cewa har yanzu akwai yiwuwar a tattauna da Tehran.
“Eh, akwai yiwuwar tattaunawa ta faru, amma ba wani abu ba ne da muke duba a kai ba,” in ji shi.
Yaƙin ya zama batun siyasa
Rikicin ya ƙara zama wani babban batu na siyasa a Amurka yayin da ’yan ƙasar ke fuskantar ƙarin farashin man fetur da tsadar rayuwa.

Source: Twitter
Amincewar jama’a da Trump ma ta ragu sosai sakamakon rashin gamsuwa da yaƙin da kuma matsalar tsadar rayuwa da ke addabar ƙasar Amurka.
Zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka da za a gudanar ranar 3 ga Nuwamba zai tantance jam’iyyar da za ta mallaki majalisun dokokin ƙasar biyu, kuma ana kallonsa a matsayin babban gwaji ga shugabancin Trump.
Trump ya dauki alkawari ga Amurkawa
Kun ji cewa shugaban kasa Donald Trump ya yi alƙawarin raba dalar Amurka 5,000 ga kowane ɗan kasar idan jam'iyyarss ta riƙe majalisu a zaben tsakiyar wa'adi.
Trump ya bayyana wannan alƙawari ne a daren farko na taron jam'iyyar Republican domin ƙarfafa gwiwar masu ƙada ƙuri'a.
Asali: Legit.ng
