'Yan PDP da ADC Sun Koma APC, za Su Yi wa Tinubu Ruwan Kuri'u

'Yan PDP da ADC Sun Koma APC, za Su Yi wa Tinubu Ruwan Kuri'u

  • Wasu tsofaffin magoya bayan PDP da ADC a Ogun sun fara gangamin neman goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da Sanata Solomon Olamilekan Adeola
  • Kungiyar Yayi Ni Wura Alliance Movement ta ce tana shirin tattara kuri'u 100,000 ga jam'iyyar APC a zaben 2027 a jihar Ogun
  • Kungiyar ta ce mambobinta sun fito daga bangarorin siyasa daban-daban, kuma za su gudanar da gangamin ne ta hanyar tuntubar jama'a da ayyukan al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abeokuta – Wasu tsoffin magoya bayan jam'iyyun PDP da ADC a jihar Ogun sun fara gangamin neman goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sanata Solomon Olamilekan Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, a zaben 2027.

Kungiyar mai suna Yayi Ni Wura Alliance Movement (YAM) ta bayyana cewa tana da burin tattara kuri'u 100,000 ga 'yan takarar APC isa jihar a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kaico: An kashe budurwa a gidan saurayinta kan rikicin daukar cutar ƙanjamau, HIV

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

'Yan PDP, PDP sun koma APC

Punnch ta wallafa cewa Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a na kungiyar, Wasiu Adejumo, wanda aka fi sani da Westo, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Alhamis a Iwe Iroyin, Abeokuta.

Adejumo ya ce mambobin kungiyar sun fito ne daga jam'iyyu daban-daban, ciki har da APC, PDP da ADC, kafin daga bisani su hada kai domin mara wa Tinubu da Adeola baya.

Ya ce burinsu shi ne tattara akalla kuri'u 100,000 domin taimakawa wajen sake zaben Tinubu tare da goyon bayan Yayi a takararsa ta neman zama gwamnan Ogun.

Dalilin goyon bayan Yayi

A cewar Adejumo, sun yanke shawarar marawa Adeola baya ne saboda muhimmancin da yake da shi a siyasar Ogun da kuma abubuwan ci gaba da suka danganta da aikinsa a jihar.

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da neman goyon bayan jama'a domin Tinubu, Yayi da sauran 'yan takarar APC a jihar.

Kara karanta wannan

Ana hurawa Tinubu wuta ya rage kudin litar man fetur zuwa N500

Shugaban kungiyar a jihar, Akeem Shodiya, ya ce an kafa YAM ne domin tattara magoya baya ga Tinubu, Adeola da sauran 'yan takarar APC gabanin zaben 2027.

Shodiya ya ce kungiyar a bude take ga mambobin wasu jam'iyyu da ke son shiga tsarin gangaminta.

Taswirar jihar Ogun
Taswirar jihar Ogun a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

'Yan APC za su fara gangami

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa za su gudanar da gangamin a sassan jihar Ogun ta hanyar tuntubar jama'a a matakin kasa da kasa, unguwanni da al'ummomi.

Ya ce kungiyar ta yanke shawarar inda take son karkata siyasarta, tare da gayyatar masu ra'ayi iri daya daga wasu bangarorin siyasa.

Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga Tinubu da dukkan 'yan takarar APC a Ogun, ciki har da Sanata Shuaib Salisu da Olumide Osoba.

A cewar kungiyar, kuri'u 100,000 da ta sanya a gaba shi ne adadin da take fatan tattarawa a matsayin wani bangare na gangamin da take gudanarwa a fadin jihar.

APC ta yi gargadi kan Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta gargadi 'yan Najeriya kan goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, wanda ke neman takarar shugaban kasa a 2027 karkashin ADC.

Kara karanta wannan

Yadda Wike da wasu gwamnoni suka yi wa Atiku da Peter Obi gadar zare

Mai magana da yawun APC na kasa, Felix Morka, ya zargi Atiku da alaka da wasu batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa, ciki har da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da badakalar cin hanci ta Siemens..

Sai dai wadannan zarge-zarge matsaya ce da jam'iyyar da APC ta bayyana a cikin sanarwarta, yayin da Atiku ya yi watsi da zarge-zargen cin hanci da ake yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng