2027: An Fatattaki 'Yan ADC a Kaduna, Jam'iyyar Ta Fitar da Gargadi
- ADC ta yi gargadi cewa babu wata jam'iyya da za a bari tana tashin hankali ita kaɗai, bayan cewar an kai hari kan wasu mambobinta a Kaduna
- Jam'iyyar ta ce harin wani mummunan ƙara tabarbarewar harkokin siyasa ne a daidai lokacin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke fara ɗaukar zafi
- Kakakin ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce jajircewar jam'iyyar wajen gudanar da siyasa cikin lumana ba yana nufin raunin siyasa ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam'iyyar ADC ta yi kakkausan gargadi bayan ta yi zargin cewa an kai hari kan wasu daga cikin mambobinta a jihar Kaduna.
Jam'iyyar ta ce tashin hankalin da aka fara shigo da shi cikin harkokin siyasa gabanin zaɓen 2027 na iya haifar da mummunan sakamako.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa ADC ta ce harin ba abin yarda ba ne, musamman ganin cewa harkokin siyasa na zaɓen 2027 sun fara ɗaukar zafi.
Gargadin da ADC ta yi
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce bai kamata a ɗauki jajircewar jam'iyyar wajen siyasar lumana a matsayin rauni ba.
Ya ce:
“Kada kowa ya ɗauki jajircewarmu wajen shiga siyasa cikin lumana a matsayin gazawa. Babu wata jam'iyyar siyasa da za ta rika amfani da tashin hankali.
“Da zarar tashin hankali ya zama abin yarda a matsayin hanyar fafatawar siyasa, babu wanda zai iya sanin inda zai ƙare.”
Batun kama maharan
Jam'iyyar ta bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta gano wadanda suka kai harin tare da kama duk wanda ya dauki nauyin shiryawa ko ɗaukar nauyin lamarin.
ADC ta ce:
“Wannan shi ya sa dole hukumomin tsaro su dauki mataki yanzu. Dole a gano, a kama sannan a gurfanar da wadanda ke da hannu a harin, da kuma duk wanda ya dauki nauyin shirya shi.”
Jam'iyyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga ɗan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Hon. Isa Ashiru, da sauran mambobin da lamarin ya shafa.

Source: Original
ADC ta ce ba ja da baya
Daily Post ta wallafa cewa ADC ta ce za ta ci gaba da shirya taruka da gudanar da kamfen a sassan jihar Kaduna duk da harin da aka kai wa mambobinta.
Jam'iyyar ta ce ya kamata zaben 2027 ya mayar da hankali kan bayyana ra'ayoyin siyasa da neman kuri'un jama'a, ba ta hanyar 'yan daba da tashin hankali ba.
Bataun mataimakin Uba Sani
A wani labarin, mun ruwaito cewa matakin Gwamnan Kaduna, Uba Sani, na zaɓar Jerry Adams, Kirista daga Kudancin jihar, a matsayin mataimakinsa a zaɓen gwamna na 2027 ya haifar da muhawara ta siyasa a jihar.
Zaɓin ya dawo da tsarin haɗa Musulmi da Kirista a takarar gwamna da mataimaki, wanda ya fi yawan zama ruwan dare a siyasar Kaduna tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.
Matakin ya kuma sauya tsarin takarar masu addini ɗaya da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya fara amfani da shi bayan rasuwar mataimakinsa, Barnabas Bala, wanda aka fi sani da Bantex.
Asali: Legit.ng
