Wata Sabuwa: Amnesty Ta Yi Zarge Zarge Masu Nauyi kan Gwamnatin Abba
- Amnesty International ta zargi jami’an tsaro da kamawa, tsarewa da tsoratar da wasu masu sukar gwamnatin Kano saboda kalamai da rubuce-rubucen kafafen sada zumunta
- Ƙungiyar ta ambaci Abba Ibrahim Kofar Nasarawa, wanda aka fi sani da Aiha K Nass, tana cewa ya kasance a tsare tun watan Agusta
- Gwamnatin Kano ta yi watsi da zarge-zargen Amnesty, tana mai cewa bayanan ƙungiyar sun kasance masu bangaranci kuma ba su nuna cikakken yanayin lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Ƙungiyar Amnesty International ta nuna damuwa kan zargin kamawa, tsarewa da kuma tsoratar da masu sukar gwamnatin Jihar Kano.
Kungiyar ta bayyana cewa hakan na haifar da fargaba tare da takaita ’yancin faɗar albarkacin baki.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Alhamis, 24 ga watan Satumban 2026 a shafinta na X.
A cikin sanarwar ƙungiyar ta yi zargin cewa an kama ko kuma gayyaci wasu mutane da hukumomin tsaro saboda kalaman da suka yi kan Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma rubuce-rubucen da suka wallafa a kafafen sada zumunta.
Amnesty ta ambaci Aiha K Nass
Amnesty ta fi nuna damuwa kan Abba Ibrahim Kofar Nasarawa, wanda aka fi sani da Aiha K Nass.
Ƙungiyar ta ce Abba Ibrahim Kofar Nasarawa ya kasance a tsare tun watan Agusta, ko da yake ba ta bayyana cikakken bayani kan dalilin tsare shi ba a cikin sanarwar.
Ta kuma ambaci Murtala Muhammad Dawanau, tana zargin cewa an tsare shi ne saboda wani sharhi da ya yi a Facebook.
Haka kuma, Amnesty ta ce an kama Fatima Dayyabu, aka gurfanar da ita a gaban kotu sannan aka ci tararta saboda sukar gwamnatin jihar.
Jerin mutanen da Amnesty ta ambata
Sauran mutanen da ƙungiyar ta lissafa sun haɗa da Maryam Usman, wadda aka fi sani da Golden Queen; Muhammad Ahmad; Hafsat Muhammad Sauwama Kauwama; Khadija Garba Kadnass; Ismail Hassan Hussain Lajin Dala; da Isa Zanna Isa.
Amnesty ta kuma yi zargin cewa Zaidu Magaji ya fuskanci barazana da tsoratarwa.
Ƙungiyar ta ce irin waɗannan matakai na nuna abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da matsa wa ’yan adawa da magoya bayansu lamba, tare da takaita ’yancin faɗar albarkacin baki a Kano.
Amnesty ta ce jama'a na da damar sukar gwamnati
Amnesty ta jaddada cewa ’yan ƙasa na da ’yancin sukar zababbun shugabanni, tana kira ga gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su mutunta ’yancin faɗar albarkacin baki da na yin tarayya.
“Yana cikin cikakken haƙƙin jama’a su soki shugaban ƙasa ko gwamna. Babu wanda ya fi ƙarfin suka, komai matsayinsa. Kama masu suka abin da ba za a amince da shi ba ne a cikin al’umma mai ’yanci,” in ji ƙungiyar.
Gwamnatin Kano ta yi watsi da zargin
Sai dai gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da zarge-zargen da kungiyar Amnesty International ta yi a kanta.
Gwamnatin ta bayyana bayanan ƙungiyar a matsayin rahoto mai bangaranci da kuma mai yaudarar fahimtar jama’a.

Source: Original
Gwamna Abba ya yi ta'aziyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Alhaji Sani Lawan Kofar Mata.
Gwamna Abba ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘yan uwa, abokan hulɗa da al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Sani Lawan Kofar Mata.
Asali: Legit.ng


