Latest
Duk da ficewar wasu jiga-jiganta saboda rikicin zaɓen fitar da gwani, jam'iyyar APC ta ci gaba da ƙarfafa rinjayenta ta hanyar nasarori da sauya sheƙa.
Allah ya yi wa tsohon kwamishina a gwamnatin Inuwa Yahaya rasuwa. Marigayin ya asu ne bayan jinyar rashin lafiya. Gwamna Inuwa Yahaya ya mika sakon ta'aziiyarsa.
Yayin da ake ta shirye-shiryen zaben shekarar 2027, ana ganin akwai wasu lamuran siyasa da har yanzu ba a kai ga warware su ba da ake ganin suna da tasiri.
Wasu 'yan Najeriya da suka ƙi barin Afirka ta Kudu bayan wa'adin 30 ga Yunin shekarar 2026 sun ɗauki makamai domin kare kansu yayin rikicin ƙin baƙi.
Rahotanni sun nuna cewa jama'a sun taru sun yi jan'izar magajin garin Kulodo, babban dansa da wasu mutane 4 da aka kashe a harin 'yan bindiga a Sakkwato.
A labarin nan, za a ji manyan labarai da suka faru tare da jawo cece-kuce a fadin Najeriya inda aka dura a kan gwamnatin Tinubu game da wasu daga cikinsu.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya ce matsalar yunwa da ke kara katutu a Arewacin Najeriya abin damuwa ne matuka, ya nemi a kara himma.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kai wani hari wata unguwa da ke kan iyakar Abuja da Nasarawa da tsakar daren ranar Juma'a.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da ceto wadanda yan bindiga suka yi garkuwa da su a coci a jihar Ekiti, sun ce mutum daya ya rasa ransa a hannun masu garkuwa.
Masu zafi
Samu kari