Siyasar Arewa: Yusuf Buhari da Ƴaƴan Manyan Mutane 4 da Za Su Fito Takara a 2027
Katsina - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, ƴaƴan wasu fitattun mutane da suka haɗa da tsofaffin shugabannin ƙasa, gwamnoni, da sarakuna sun fara fitowa fili domin neman muƙaman siyasa daban-daban.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wannan yanayi, wanda masana ke gani a matsayin yunƙurin dorewar tasirin ahali a fagen mulki, ya mamaye garuruwa da dama, tun daga Daura har zuwa Kano.

Source: Facebook
2027: 'Ya'yan manyan mutane da za su fito takara
Ga jerin wasu daga cikin waɗannan ƴaƴan manyan mutane da suka tabbatar da sha'awar su ta yin takara a 2027, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
1. Muhammad Sani Abacha (PDP)
Ɗan tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha, ba baƙon fuska ba ne a fagen siyasar Kano. Muhammad, wanda babban jigo ne a jam’iyyar PDP, ya sake ƙulla ɗamara domin takarar gwamnan Kano a 2027.
Duk da samun tikitin PDP a 2023 da kuma takarar da ya yi a ƙarƙashin CPC a 2011, damar zama lamba daya a jihar Kano na ci gaba da kuɓuce masa.
Rahoto ya nuna cewa Muhammad Sani Abacha yana ci gaba da zama mai tasiri a siyasar Kano, inda yake cin gajiyar tasirin ahalinsa da kuma dumbin magoya bayan PDP.
2. Umar Abdullahi Ganduje (APC)

Source: Facebook
Umar Ganduje wanda aka fi sani da “Abba Ganduje,” shi ne ɗan tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Rahoto ya nuna cewa Abba Ganduje yana neman kujerar majalisar wakilai ta mazaɓar Rimin Gado/Dawakin Tofa/Tofa.
Idan ba a manta ba, The Cable ta ruwaito cewa Abba Ganduje ya sha kasa a zaben 2023 a hannun Tijjani Abdulkadir Jobe na jam'iyyar NNPP.
Ganin cewa Jobe ya koma APC, zaɓen fitar da gwani tsakanin mai ci da “yariman” gidan Ganduje na ɗaya daga cikin zaɓukan da za a fi sanya wa ido a jihar Kano.
3. Muhammad Daha Umar Faruk

Source: Facebook
Mai riƙe da sarautar Danburam na Daura, Muhammad Daha Umar Faruk ba ɗan siyasa ba ne kawai; shi ne mai jiran gadon sarautar Daura.
A matsayinsa na babban ɗan Sarkin Daura, HRH Faruk Umar Faruk, shigar sa takara, don wakiltar mazaɓar Baure/Zango a majalisar tarayya ya girgiza tsarin siyasar Daura, in ji rahoton Trust TV.
Yayin da ya ce ya amsa “kiraye-kirayen jama’a,” Danburam ya nuna kansa a matsayin ɗan takarar talakawa, kodayake bai bayyana jam’iyyar da zai yi amfani da ita ba.
4. Yusuf Muhammadu Buhari (APC)

Source: Facebook
Wataƙila babu sunan da ya kai nauyin Muhammadu Buhari a Katsina, ko ma a Najeriya. Goyon bayan da aka fara nunawa ɗan tsohon shugaban ƙasar domin neman kujerar majalisar tarayya ta mazaɓar Daura/Sandamu/Mai’adua ya isa hujja.
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na X (wanda aka sani da Twitter a da).
Bashir Ahmad ya bayyana cewa wannan matakin da ɗan gidan marigayi tsohon shugaban ƙasar ya dauka ya biyo bayan doguwar shawara da aka yi da manyan 'yan siyasa, in ji rahoton Legit Hausa.
Yayin da magoya bayansa ke ganinsa a matsayin magajin siyasar mahaifinsa kuma wanda ya dace da tsarin 'Not Too Young To Run', a gefe daya kuma jiga-jigan APC sun fara ja-in-ja a kan wannan takara.
5. Mubarak Ahmad-Gumi (APC)

Source: Facebook
A cikin haɗin gwiwar tasirin addini da siyasa, ɗan fitaccen malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi, yana neman kujera a majalisar dokoki ta jihar Kaduna (Doka/Gabasawa), in ji rahoton Premium Times.
A halin yanzu Mubarak yana aiki a matsayin mai tallafa wa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, inda ake hasahen tasirin mahaifinsa a cikin al'umma zai iya kai shi ga nasarar a zaɓen mai zuwa.
A ganin Mubarak Ahmad-Gumi, ya kamata matasa su daina tsaya wa a kafafen sada zumunta, su shiga siyasa domin kawo sauyi mai ma’ana a cikin al'umma.
Sauran 'ya 'yan manyan da ake ganin za su iya shiga takara sun hada da: Abdulaziz Umar Ganduje, Shamsuddeen Bala Mohammed da sauransu.
'Babu laifi a takarar ƴaƴan masu hannu da shuni'
Farfesa Kamilu Sani Fagge na sashen kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana cewa babu wani laifi ga ƴaƴan ƴan siyasa, attajirai, sarakuna, da malamai su tsaya takarar muƙaman zaɓe.
Da yake magana kan yawaitar ƴaƴan manya a siyasa, Fagge ya bayyana cewa tsarin mulkin Najeriya ya ba kowane ɗan ƙasa haƙƙin kaɗa ƙuri’a da kuma neman zaɓe, ba tare da la’akari da matsayi, addini, ko jinsi ba.
Ya bayyana cewa damuwar tana tasowa ne kawai idan aka yi amfani da matsayin su domin danne sauran ƴan takara.
A cewarsa, dimokuradiyya tana bunƙasa ne kan adalci, kuma duk wani yunƙuri na amfani da dukiya, dangantakar sarauta, ko uban-gida domin murƙushe wasu yana gurgunta tsarin.
Rigima a APC kan takarar Yusuf Buhari
Tun da fari, mun ruwaito cewa, rikici ya barke a cikin jam’iyyar APC a Daura bayan wasu ‘yan jam’iyya sun amince da takarar Yusuf Buhari.
Hakan ya biyo bayan amincewa da dan marigayi Muhammadu Buhari a matsayin ɗan takara a majalisar wakilai daga jihar Katsina.
Wasu manyan jiga-jigan APC daga ƙananan hukumomi biyar sun yi fatali da zargin ɗora ‘yan takara, suna cewa ba za su amince da hakan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



