Dalilin da Ya Sanya na Saki Matata Maimuna Pretty, Adam A Zango Ya Yi Bayani
- Jarumi Adam A. Zango ya tabbatar da rabuwarsa da matarsa, Maimuna Musa, inda ya bayyana cewa dukkansu suna da genotype iri daya
- Adam Zango ya roƙi jama'a da su guji yaɗa jita-jita, yana mai cewa ya bayyana gaskiyar ne domin sanar da masoyansa abin da ya faru
- Jarumin ya ce rabuwar ta gudana cikin mutuntawa, tare da wallafa bidiyon ranar da Maimuna ta bar gidansa cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kaduna - Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya tabbatar da cewa auren sa da Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Maimuna Pretty ya mutu.
Adam Zango ya yi bayani cewa auren ya mutu ne kasancewar dukkansu suna da genotype AS, kuma daya ne daga cikin dalilan da suka kawo ƙarshen auren.
Adam Zango ya yi bayani kan genotype
Jarumin ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, bayan jita-jitar da ta bazu kan rabuwar tasu.
A cewar Adam A. Zango, gaskiya ne cewa shi da tsohuwar matarsa sun gano cewa suna da irin genotype ɗaya.
Ya ce shi genotype ɗinsa AS ne, haka ita ma Maimuna tana da genotype AS.
Jarumin ya ce ya ga ya dace ya bayyana wannan bayani domin jama'a su san gaskiyar abin da ya faru, maimakon ci gaba da yaɗa jita-jita ko bayanan da ba su da tushe.
Ya roƙi a mutunta sirrin lamarin
Adam A. Zango ya buƙaci masoyansa da sauran jama'a da kada su mayar da rabuwar aurensu abin ce-ce-ku-ce.
Ya ce manufarsa ba wai zargin wani ko tona sirri ba ce, illa dai sanar da masoyansa dalilin da ya sa aurensu ya zo ƙarshe.
Jarumin ya ƙara da cewa yana son a mutunta sirri da mutuncin dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa.
Bidiyon ranar da Maimuna ta bar gida
A wani mataki, Adam A. Zango ya wallafa wani bidiyo da ya ce an ɗauke shi a ranar da Maimuna Musa ta tattara kayanta ta bar gidansa.
A cewarsa, bidiyon ya nuna cewa ta bar gidan cikin farin ciki da kwanciyar hankali, abin da ya nuna cewa rabuwar tasu ta gudana cikin mutuntawa ba tare da wata hayaniya ko rikici ba.
Sai dai jarumin bai bayyana wasu ƙarin bayanai kan rabuwar auren ba, yana mai jaddada buƙatarsa ga jama'a da su mutunta sirrin lamarin tare da gujewa yaɗa bayanan da ba su da tushe.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Asali: Legit.ng

