Pantami, Gwamnoni, Yusuf Buhari Sun Isa Borno Auren 'Ya'yan Gwamna Zulum 4

Pantami, Gwamnoni, Yusuf Buhari Sun Isa Borno Auren 'Ya'yan Gwamna Zulum 4

  • Jihar Borno na cigaba da karbar manyan baki yayin da ake shirye-shiryen daura auren 'ya'yan gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum
  • Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya isa jihar Borno, inda ya gabatar da nasiha game da rayuwar aure a daren ranar Juma'a
  • Tuni dai manyan baki suka fara isa jihar Borno, inda aka hango dan marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf a cikin wata tawaga tare da Pantami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bukaci ma’aurata su gina aurensu kan soyayya, rahama da hakuri.

Pantami ya yi wannan kira ne a daren Juma’a a Maiduguri, yayin wani taron gab da aure da aka shirya wa ‘ya’ya hudu na Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Kara karanta wannan

"Za a kore shi"; Amaechi ya kalubalanci Tinubu ya yi abu 1 kan zaben 2027

Sheikh Pantami wajen daurin auren 'ya'yan Babagana Zulum
Isa Ali Pantami yayin nasiha wajen taron auren 'ya'yan gwamna Babagana Zulum. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Pantami ya sanar da cewa ‘ya’yan na Zulum hudu sun hada da Umara, Mamman, Abba da Aisha.

Yusuf Buhari da baki sun isa Borno

Rahotanni sun nuna cewa bikin daurin auren 'ya'yan Farfesa Zulum ya ja hankalin jama’a a Maiduguri, inda ‘yan uwa, malamai da manyan baki suka hallara.

A wasu hotuna da aka fitar, Legit Hausa ta hango gwamnonin Zamfara, Kebbi, Sokoto da kuma Ministan noma, Abubakar Kyari da Yusuf Muhammadu Buhari a cikin manyan baki.

Gwamnoni wajen daurin auren 'ya'yan gwamna Babagana Zulum
Sheikh Isa Pantami, gwamnoni da wasu baki a wajen taron auren 'ya'yan gwamna Babagana Zulum. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Nasihar Pantami ga 'ya'yan Zulum

Da yake jawabi a wajen taron, Sheikh Pantami ya bayyana muhimmancin aure a bangaren addini da zamantakewa, yana mai cewa aure na taimakawa wajen cika rabin addini.

Ya kara da cewa ya ce aure na samar da natsuwa da kwanciyar hankali, jawo lada daga Allah, gina iyalai nagari da kuma samar da al’umma mai tarbiyya.

Kara karanta wannan

Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa

A cewarsa, soyayya a cikin aure na bayyana wajen nuna kauna ta gaskiya, kulawa da kusanci, yana mai jaddada cewa zamantakewar aure da ba ta jawo soyayya da rahama ba, ba ta cika manufarta ba.

Magana kan dorewar zaman aure

Malamin ya bayyana cewa amfanin aure ba zai dore ba sai da hakuri, wanda ke karfafa juriya, yafiya, dagewa da kuma girmama juna tsakanin ma’aurata.

Pantami ya ce iyalai masu nagarta na samuwa ne sakamakon hakuri, yana mai cewa akwai bukatar kowane mutum ya dage da yin hakuri.

Muslim News ta rahoto ya ce:

“Iyayenmu sun yi hakuri yayin zaman aure har suka samar da mu.”

Malamin addinin ya nuna damuwa kan karuwar rabuwar aure a tsakanin matasa, yana danganta yawan gazawar aure a farkon shekaru da rashin hakuri da rashin juriya.

Sheikh Pantami da Yusuf Buhari
Isa Ali Pantami da Yusuf Buhari a wajen taron auren 'ya'yan gwamna Babagana Zulum. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Ya bukaci matasa su rungumi wadatar zuci, yafiya da juriya domin gina gidaje masu dorewa:

“Dole ne mu shiryar da matasanmu kan juriya, wadatar zuci, yafiya, girmama juna, dagewa da kuma soyayya.”

An fasa daura aure kan Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa wani uba ya fasa daurawa wani matashi auren 'yarsa saboda matashin yana tallata shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Yobe ya tara malamai 800, za su dukufa wajen yi wa Tinubu addu'a

Rahotanni sun nuna cewa mahaifin ya duba irin abubuwan da matashin da ke neman auren 'yarsa ke wallafawa game da Tinubu a intanet.

Matakin da mahaifin budurwar ya dauka ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwa tsakanin matasa a Arewaci da Kudancin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng