Jam'iyyar APC a Kano Ta Daina Goyon Bayan Tinubu? Magana Ta Fito

Jam'iyyar APC a Kano Ta Daina Goyon Bayan Tinubu? Magana Ta Fito

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta fito ta yi magana kan batun janye goyon bayanta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • APC ta bayyana cewa kungiyar da ta yi batun janye goyon baya ga Tinubu, ba sananna ba ce a cikinta
  • Jam'iyyar ta kuma jaddada goyon bayanta ga shugaban kasar tare da amincewa da manufofinsa na ci gaban kasa

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi martani kan batun janye goyon bayanta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

APC ta ƙaryata wata sanarwa da wata ƙungiya mai suna Arewa APC Forum reshen jihar Kano ta fitar, tana iƙirarin janye goyon baya ga takarar tazarce ta Shugaba Bola Tinubu.

APC ta yi martani kan daina goyon bayan Tinubu
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na Kano, Auwalu Abdullahi, ya fitar ranar Asabar, 18 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027

Me APC ta ce kan janye goyon baya ga Tinubu?

APC ta bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, yaudarar jama’a, kuma wani shiri ne da aka yi domin ɓata sunan jam’iyyar.

Jam’iyyar ta jaddada cewa babu wani sashe na jam’iyyar APC da tsarin mulki ya ba damar ɗaukar wannan mataki, inda ta nanata cewa reshen jihar Kano yana nan daram kan goyon bayan Tinubu da gwamnatinsa.

"APC a Kano tana sane da yunƙurin wasu mutane da wasu ƙungiyoyi marasa tushe na ƙoƙarin haifar da rudani da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar."
“Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa wannan ƙungiya da ake kira 'forum' ba a san ta ba a tsarin jam’iyyar, kuma ba ta wakiltar ra’ayoyin mambobin APC a jihar Kano.”

- Auwal Abdullahi

APC za ta ci gaba da goyon bayan Tinubu

Jam’iyyar ta ƙara jaddada amincewarta ga jagorancin Tinubu, inda ta lura cewa gwamnatinsa tana mai da hankali kan samar da kyakkyawan shugabanci, gyaran tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa, shafin Dailyreport ya dauko labarin.

Kara karanta wannan

Gabanin 2027, ADC ta fada wa Tinubu maganar da za ta jefa masa tsoron 'yan adawa

APC ta musanta janye goyon baya ga Tinubu
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Umar Doguwa Hoto: Abba Rabiu Gwarzo
Source: Facebook

APC ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Umar Doguwa, ta buƙaci mambobin jam’iyyar da sauran jama’a da su yi watsi da wannan sanarwa baki ɗayanta, tana mai bayyana ta a matsayin aikin masu son tada zaune tsaye domin haifar da takaddama maras amfani.

Sanarwar ta kammala da nanata haɗin kan jam’iyyar da kuma goyon bayanta ga kyakkyawar manufar Tinubu ga Najeriya.

Tinubu ya yi martani ga 'yan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi martani ga 'yan adawa da ke sukar gwamnatinsa.

Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai jin tsoron wadanda ke shirin cewa za su kwace mulkin Najeriya daga hannun shi a zaben shekarar 2027.

Hakazalika, ya nuna cewa wadanda ke kokarin karbe mulki a hannun shi a 2027 suna da tarihin gazawa, yana mai cewa hakan na nuna rashin kwarewarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng