An Hana Musulma Shiga JAMB saboda Saka Hijabi, Sheikh Gumi Ya Yi Magana

An Hana Musulma Shiga JAMB saboda Saka Hijabi, Sheikh Gumi Ya Yi Magana

  • Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan zargin hana wata daliba shiga dakin rubuta JAMB
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wata cibiyar da ake rubuta jarrabawar a Oyo, ina ana hana dalibar shiga ciki saboda sanya hijabi
  • Kakakin hukumar JAMB na kasa, Fabian Benjamin ya yi karin haske kan abubuwan da suka faru da matakin da aka dauka a hukumance

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bukaci a gudanar da bincike kan zargin cewa cibiya ta hana wata daliba rubuta jarrabawar UTME saboda sanya hijabi.

Hakan na zuwa ne yayin da jama'a da dama suka rika nuna damuwa kan zargin hana dalibar shiga wajen rubuta jarrabawar saboda wariyar addini.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi
Sheikh Ahmad Gumi yana wa'azi a Kaduna. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Kiran Sheikh Ahmad Gumi ga JAMB

Sheikh Gumi ya yi wannan kira ne a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Asabar, bayan wata bidiyo da ke nuna lamarin ta yadu a shafukan sada zumunta.

Yayin magana ne bayan ganin wasu jami’an tsaro a cibiyar rubuta JAMB da ke cikin wata makaranta suna nuna kamar suna hana wata daliba mai hijabi shiga yayin bincike, alhali suna barin wasu dalibai da ba su sanya hijabi ba su shiga.

Gumi ya ce irin wannan hali bai kamata a amince da shi ba:

“An ruwaito cewa wata makaranta a Abuja ta hana mai hijabi shiga dakin jarrabawar JAMB.
“Wannan abu na bukatar bincike, kuma ya kamata a hukunta cibiyar. Wane irin wariya ne wannan a kasarmu? Bai kamata a taba amincewa da hakan ba.”

Sai dai duk da Sheikh Gumi ya ce a Abuja abin ya faru, The Sun ta wallafa cewa cewa an samu irin wannan lamari a cibiyar CBT ta Esther Oshikoya a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Burundi: An samu gawar minista a mota, an masa mummunan rauni a kai

Daliba mai rubuta jamb da hijabi
Daliba mai hijabi da ake ce an hana shiga rubuta JAMB. Hoto: Northern Magazine
Source: Facebook

Bayanin JAMB kan daliba mai hijabi

Da yake mayar da martani a wata sanarwa, kakakin JAMB, Fabian Benjamin, ya ce hukumar ta yi Allah-wadai da lamarin, yana mai cewa hukumar na mutunta akidu da al’adun dukkan ‘yan Najeriya.

Ya ce:

“Ta hanyar hanyoyin sa ido da muke da su, hukumar ta lura da abin da ya faru yayin tantance dalibai a zangon farko na jarrabawar ranar Alhamis.”
“Hukumar ta dauki matakin gaggawa ta hanyar kiran jami’in wucin gadi da ke da hannu a lamarin tare da ba da umarni cewa kada a tilasta wa duk wata daliba mai hijabi cire shi ko sauya shi.”

Kakakin ya kuma bayyana cewa ba manufar hukumar ba ce, wani jami’in wucin gadi ne da ya wuce gona da iri, wanda bai bi ka’idojin da hukumar ta gindaya dangane da suturar addini ta dalibai ba.

Ga bidiyon dalibar da Maliq ya wallafa a X:

Kara karanta wannan

Kaddamar da sababbin jiragen kasa a Legas ya harzuka 'yan Arewa

Maganar Ahmad Gumi kan soke shari'a

A wani labarin, kun ji cewa malamin Musulunci ya yi martani kan kiran da aka fara daga Amurka domin neman soke shari'ar Musulunci a Najeriya.

Ya bayyana cewa Shari'a dama ce da kundin tsari mulkin Najeriya ya ba dukkan Musulmi kuma babu wanda zai iya kwace musu shi.

Wasu 'yan majalisar Amurka ne suka yi kira da hakan bayan zarge-zargen kisan Kiristoci da aka ta yadawa a Najeriya tun karshe-karshen 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng