Latest
A labarin nan, za a ji cewa jam'iyya mai mulki a Najeriya ta fara shirin tsayar da ƴan takarar da za su fafata da ƴan adawa a babban zaben 2027 da ke karatowa.
Shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya yi kira ga Leke Abejide da Nafiu Bala da su tsaya su tarwatsa jam'iyyar adawa ta ADC.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito ya yi martani kan sukar da Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa gwamnatinsa. Ya ce kowa yana yin kuskure.
A yayin da ake sa ran ci gaba da zaman sulhu tsakanin Amurka da Iran a Pakistan, shugaba Donald Trump ya yi barazana a kan kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.
A labarin nan, za s ji cewa maharan Boko Haram sun fitar da bidiyo cike da nuna raini da rashin kunya ga gwamnatin Najeriya bayan sace mutane a Borno.
Tsofaffin ƴan sanda sun rufe ƙofar fadar shugaban ƙasa a Abuja yau 20 ga Afrilu, don neman Shugaba Tinubu ya sa hannu kan dokar fitar da su daga tsarin fanshon CPS.
Kasar Musulunci ta Iran ta dage cewa ba za ta yarda da matakan da Amurka ta dauka kanta ba, ta ce halayen kasar ne suka jawo cikas a tattaunawar sulhu.
'Yan bindiga sun kashe sojoji uku da ƴan banga a Kemanji, jihar Kwara, sannan suka sace motar yaƙi da makamai. Majiyoyi sun bayyana yadda maharan suka kai farmakin.
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce bayan Kwankwaso, akwai kusoshin siyasa da za su hade da Atiku, Peter Obi da sauran yan hadaka.
Masu zafi
Samu kari